Rayuwar Marigayi Yusuf Maitama Sule, Ɗan Masanin Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Sanin mutum sai Allah! Daga cikin mutane, akwai waɗanda Allah ke yi wa baiwar da bayyana ta ke da matuƙar wahala. Irin waɗannan mutane, rayuwarsu cike ta ke da darrusan da za a iya koya. Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗan Masanin Kano, ɗaya ne daga cikin irin waɗannan mutane. Mutum ne mai ilimin addini da kuma na zamani.

Allah ya yi masa baiwa da haƙuri, gaskiya, riƙon amana, cika alƙawari, sada zumunci, yafiya, barkwanci, dogaro da kai, da kuma sadaukar da kai. Mutum ne ɗan kishin ƙasa, mai son ganin jama’a sun ci gaba, mai son zaman lafiya da haɗin kai, ga kuma uwa-uba, abin da ya zama gagarabadau a kai, wato fasahar zance da kuma iya magana.

Alhaji Yusuf Maitama Sule, malamin makaranta ne, ɗan siyasa sannan kuma basarake. Tabbas, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ciyar da ɗaiɗaikun mutane gaba har zuwa kan gwamnatin tarayya. Da shi aka yi fafutikar ƙwatar ’yanci da kuma ganin yunƙurin tabbatar da haɗin kan ƙasa da ɗorewar zamanta a matsayin ƙasa guda.

Alhaji Yusuf, ya yi aiki da sarakunan Kano biyar, da kuma gwamnan Kano Audu Baqo, sannan kuma ya yi aiki da shugabannin Nijeriya tun daga kan Dr. Nmandi Azikwe, har zuwa hawan shugaba Buhari na biyu (2017), wasu lokutan kai tsaye ta hanyar riƙe wani muƙami a cikin gwamnati, wasu lokutan kuma a bayan fage kamar yadda ta faru a zamanin Janar Muhammadu Sani Abacha.

Haka nan kuma a dimokuraɗiyyance, da shi aka kafa jamhuriyyar farko, ta biyu, ta uku, da ta huɗu da mu ke ciki a yanzu. Yana da ƙwarewa a fannin siyasa ta gida da kuma wajen Nijeriya.

Haƙiƙa, na san wannan teku, duk wanda ya shige ta, zai kamfacin ruwan da zai ya sha ya yi wanka. Ina taya mai karatu murnar shiga wannan makaranta da za a kwashi darrusan rayuwa a ɓagas. A sha karatu lafiya.

Haihuwa da salsalarsa:

An haife shi a garin Kano cikin unguwar Yola, a shekarar 1929. Sunansa na yanka shi ne Yusuf, sunan da Madawakin Kano Mahmudu ya buƙaci a saka masa domin ya maye gurbin sunan mahaifinsa da shi.

Madawaki Mahmudu, ya riqa kiransa da suna Abbana. Su kuwa sauran jama’ar fada, suna kiransa da suna Maitama, saboda al-kunya, don gujewa kiran sunan mahaifin Madawaki Mahmudu kai tsaye.

Wannan suna kuma na Maitama, ya samo asali ne daga Galadiman Kano Yusuf, wanda a lokacin da ya ke kan kujerar Galadiman Kano, an yi yaƙin da ya sabauta yawan amfani da makaman da aka samar daga tama; ita kuwa tama, sidanari ce da ake haɗa ƙarfe da ita. Saboda haka, sai aka riƙa kiran shi Galadima da sunan Maitama.

Da aka samu Yusufu, sai kuma aka sake ara masa wancan suna. Saboda haka, sai sunansa ya zama Yusuf Maitama. Sunan mahaifnsa kuma Sule, saboda haka cikakken sunansa shi ne Yusuf Maitama Sule.

Mahaifin Yusuf Maitama, wato Sule, ɗa ne ga Ahmadu, wanda shi kuma Ahmadu Bafulatani ne daga garin Maraɗi da ke cikin Nijar a yau. Ana zaton cewa ko dai an kamo shi Ahmadu ne a lokacin yaƙi, ko kuma an sayo shi ne aka kawo garin Kano.

Ahmadu ya kasance makusanci ga Madawaki Ƙwairanga (1894); wato Madakin Sarkin Kano Aliyu ɗan Abdullahi (Alu mai Sango) 1894 – 1903. Ahmadu da Ƙwairanga aminan juna ne tun kafin zamowar shi Ƙwairanga Madawaki. Duk gurin da aka ga zara, to a ga wata. Ko a fagen daga suna tare. Haka nan kakarsa mai suna Hadiza, mutumiyar Ningi ce da mahara suka kamo ta zuwa Kano, a lokacin suna tsaka da bikin wata ƙawarsu.

A lokacin gudun hijira zuwa Dutsin Bima, Sule yana goye aka yi wannan hijira da shi. Shi Ahmadu, mahaifin Sule, wato kakan Yusufu ta wajen mahaifinsa, shi ne Wazirin Madawakin Kano Ƙwairanga. Shi kuma Sule, wato mahaifin Yusufu, shi ne Ɗanmurin Madawakin Kano Mahmuda, daga baya kuma ya zama Turakin Yola a zamanin Madawaki Shehu.

Sunan mahaifiyarsa Hauwa, wacce ita kuma ’ya ce a wajen Isyaku. Shi kuma Isyaku, shuwa ne daga Chadi. Shi ma dai kamo shi aka yi a lokacin farmakin Barno, da aka yi a cikin shekarar 1890, daga nan aka kawo shi garin qunci, daga baya kuma ya tsinci kansa cikin ayarin bayin Madawakin Kano wanda ya zamar wa Madawaki Hussaini Babban Zagi, har zuwa zamanin Madawaki Mahmudu. Ita kuwa kakarsa ta wajen mahaifiya, ’ya ce a wajen limamin Dawakin Tofa, gundumar da a koda wane lokaci ta ke ƙarƙashin hakimcin Madawakin Kano.

Ɗan Masanin Kano:

A cikin shekarar 1954, bayan zamowar Alhaji Yusuf Maitama Sule, jami’in yaɗa labarai na hukumar gargajiya ta Kano, sarkin Kano Muhammadu Sanusi na farko (1953 – 1963), ya buƙaci Alhaji Yusuf Maitama Sule, da ya zaɓi dukkan sarautar da ya ke so a naɗa shi, ba tare da ya nema ba.

Bayan samun wannan tayi da Alhaji Yusuf Maitama Sule ya yi daga wajen sarki, sai ya nemi shawara daga Malam Ahmad Mettidan, wanda shi kuma a lokacin ma’aikaci ne a gidan radiyon tarayya (Nigerian Broadcasting Corporation). Inda ya ba bashi shawara cewa, ya zaɓi sarautar Ɗanmasani, wacce ita kuma wannan sarauta ta Ɗanmasani, asalin ta daga Katsina ne. Tun da farko akwai wani waliyyi daga cikin waliyyan Katsina guda huɗu mai wannan sunan.

Shi Wali Ɗanmasani, aikin sa a fadar Katsina shi ne jagorantar sarki da masarautar Katsina a kan al’amuran addini. Bayan rasuwar wannan waliyi kuma, sai sunan ya zama sarauta, aka naɗa ɗansa a kan wannan kujera, sannan aka ci gaba da kiransa da malam Ɗanmasani.

Gwagwarmayar siyasa da fafutikar ’yanci:

Tun lokacin da ya ke karatu a Kwaleji, Alhaji Yusuf Maitama Sule, yana da ra’ayin baiwa jama’arsa da ƙasarsa gudunmawa, amma sai dai, ba shi da cikakkiyar masaniya game da harkar siyasa. Har sai a cikin shekarar 1948, a lokacin dawowarsa gida daga Legas, bayan zuwansu ziyara tare da sauran ɗaliban Babbar kwalejin elimantaren horar da malamai da ke Zariya (Higher Elementary Teachers College, Zaria), ya haɗu da shugaban Nijeriya na farko, Dr. Nmandi Azikwe a jirgi, wanda suka tattauna da shi kan abubuwan da suka shafi siyasa.

Wannan tattaunawa, ita ce farkon abin da ya fara jan hankalin Maitama zuwa harkokin siyasa. Tun daga wannan lokaci, ake ta fafatawa da shi.

Ɗan siyasa ne shi a gida da wajen Nijeriya. Ya bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan al’ummu, garuruwa, ƙasashe a faɗin duniya.

Tabbas, wannan shi ne Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗan Masanin Kano. Malamin makaranta, Ɗansiyasa, kuma basarake.