Red Cross ta bada tallafin kuɗi don rage raɗaɗin talauci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya (NRCS) ta ce, za ta fara shirin raba kuɗaɗe ga mutane miliyan 2.5 a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar Nijeriya a ƙoƙarinta na magance yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

Mista Anthony Abah, Sakataren Reshen NRCS Benuwai, ya ba da wannan umarni a Makurdi yayin wani taron horar da ma’aikata da masu sa kai kan yadda za a raba kuɗaɗen shirin na CTP.

Ya ƙara da cewa, “a shekarar 2022, al’umma na son fara shirinta na daƙile ko ma kauce wa illar yunwa da rashin abinci mai gina jiki a jihohin Benuwai, Neja, Nasarawa, Katsina, Zamfara, Kebbi da Sokoto.”

Ya ce, za mu a ilmantar da ma’aikata da masu aikin sa kai kan shirin ‘Matsalar Yunwa, Sadarwar Jama’a da Ba da Lamuni’ (CEA).

Sauran, in ji shi, kariya ce ta jinsi da haɗa kai, tun da an koya wa masu aikin sa kai hanyoyin da za a ba da kuɗi.

A cewarsa, an shirya hakan ne don magance matsalar yunwa da kuma samar da abinci mai jina jiki a tsakanin al’umma.

Ya ce, manufar ƙungiyar kuma ita ce rage wahalhalun da ke addabar marasa galihu da suka haɗa da waɗanda bala’o’i, annoba da kuma rikice-rikice suka shafa.

Abah ya ce, ƙungiyar na yi wa al’ummar da ke fama da talauci hidima a birane da karkara, waɗanda suka haɗa da mata, yara, tsofaffi, waɗanda suka rasa matsugunansu da sauran marasa galihu.