Daga USMAN KAROFI
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ya soki matakin da ofishin jakadancin Kanada ya ɗauka na hana babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, da wasu manyan jami’an soja takardar izinin shiga ƙasar. Yayin wata lacca a Abuja, Ribadu ya bayyana matakin a matsayin rashin mutunci, yana mai cewa, “Su je za su gani.”
Janar Musa, wanda aka gayyata zuwa Kanada domin wani biki na girmamawa ga jaruman da suka yi yaƙi, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu jami’an aka basu biza, yayin da wasu aka hana. Ya ce hakan wata ishara ce ga Najeriya da ta ƙara ƙarfafa ‘yancinta da matsayinta a duniya. Ribadu ya goyi bayan Musa, yana mai jaddada buƙatar Nijeriya ta dogara da kanta kuma kada a ci gaba da wulakanta ta a fagen diflomasiyya.
Duk da wannan matsala, Ribadu ya jinjinawa sojojin Nijeriya kan ƙoƙarin su na yaƙi da rashin tsaro a ƙasar. Ya yaba da jagorancin Musa kuma ya tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya tana nan daram wajen inganta tsaro da kare martabar ƙasar a idon duniya. Wannan lamarin ya tayar da muhawara kan dangantakar diflomasiyya tsakanin Nijeriya da Kanada, inda wasu ke kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin martani.