Rigimar Majalisar Dokokin Nasarawa: Mambobin ɓangaren Ogazi na canja sheƙa zuwa ɓangaren Balarabe

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ne Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta tsunduma cikin rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa jim kaɗan bayan zaɓen kujeral Kakakin Majalisar wanda aka so a gudanar a lokacin amma bai yu ba, inda a ƙarshe aka samu ɓangarori 2 tsakanin mambobin majalisar inda wasu ke goyon bayan tsohon kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi wanda ke neman zarcewa a kujerar, yayin da wasu kuma ke tare da Ogah Ogazi da shi ma yake neman hawa kujera.

Kodayake a lokacin ma fi yawan ‘yan majalisar da suka ƙunshi sabbi da tsofaffin ‘yan majalisar da aka sake zaɓa suna tare da Daniel Oga Ogazi ne.

Amma a yanzu an samu akasin haka inda kawo yanzu binciken wakilin mu ya gano cewa wasu daga cikin mambobin dake ɓangaren Ogazi ɗin na ci gaba da canja sheƙa zuwa ɓangaren kakakin majalilisar wato Ibrahim Balarabe Abdullahi.

A halin yanzu dai kawo lokaci da ake haɗa wannan rahoto kimanin mambobin daga ɓangaren Ogazi su 3 ne suka koma rukunin Balarabe.

Sabbin zuwan daga ɓangaren adawar sun haxa mamba mai wakiltar mazavar Awe ta Arewa a majalisar, Honorabul Hudu A. Hudu da mamba mai wakiltar Keffi ta Yamma, Honorabul John Ovey da wanda ke wakiltar Doma ta Kudu, Honorabul Mohammed Oyanki.

A halin yanzu dai tuni kakakin majalilisar dokokin, Ibrahim Balarabe Abdullahi ya karɓe su da hannu biyu ya kuma rantsar dasu a matsayin zaɓaɓɓun kuma cikakkun mambobin majalisar.

Har ila yau ga duka alamu binciken wakilin mu ya gano cewa Ibrahim Balarabe Abdullahi ne ainiyin kakakin majalisar dokokin don kawo yanzu kusan duka hukumomin daban-daban ciki harda gwamnatin jihar sun amince da shine a matsayin inda tuni gwamnan jihar Injiniya Abdullah Sule ya taya shi murnan zaɓinsa a matsayin kakakin majalilisar karo na uku.

Kuma gwamnatin na cigaba da hulɗa da shi ne a hukumance a kuma matakin. Kana har ila yau ga duka alamu lokaci ne kawai ya rage aga sauran mambobi ‘yan adawan daga ɓangaren Daniel Ogah Ogazi duk su dawo gun Balarabe a rantsar da su suma a matsayin ainihin kakakin su na majalisar dokokin jihar ta Nasarawa rukuni na karo na bakwai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *