Rikiɗewar siyasa zuwa ta addini da ƙabilanci a Kaduna

Yayin da jam’iyyu ke shirin tunkarar zaɓen gwamna da na ’yan majalisun dokokin jihohi a Nijeriya, wani batu da ke fitowa fili a fagen siyasar Jihar Kaduna shi ne na siyasar addini da kuma ƙabilanci.

A baya dai jihar ta sha fama da rikice-rikice masu nasaba da addini da ƙabilanci, lamarin da masana ke nan suka ce yana matuƙar janyo komawa baya ga tsarin dimokuraɗiyya.

Duk da cewa akwai masu neman takarar kujerar gwamna a jihar fiye da 10, takarar tafi zafi ne a tsakanin jam’iyyar APC da kuma PDP.

Masana harkokin siyasa a jihar dai sun fara nuna damuwa a kan yadda salon siyasar jihar ya ɗauka inda batun addini da kuma ɓangaranci ke jujjuya alkiblar siyasa a baya bayan nan a jihar.

Idan aka lura yanzu malaman addinai da kuma shugabannin majami’u sun duƙufa wajen nunawa mabiyansu cewa ga wanda za su zaba saboda shi ne zai wakilci addininsu ko kuma yankinsu.

A gaskiya a tsari na siyasa ba wannan ake dubawa ba, domin idan aka ce za a riƙa diba irin wannan, to babu inda za a je.

Muddin za a yi amfani da addini ko ƙabilanci a tsarin siyasa to za a iya fuskantar babbar illa a tsarin dimokuraɗiyyar jiha koma ƙasa.

Bin irin wannan tsari ya kan sa a hana wa mutane zaɓar wanda suke gani zai iya yi musu jagoranci da kuma kawo musu shugabanci na gari saboda an saka addini a ciki.

Haka suma shugabannin addinin idan suka sanya mutane suka zaɓi waɗanda ba su dace ba, wanda daga baya ba a samu abin da ake so ba daga wajensu, sai su zo suna jin kunyar mutane, saboda sun sa su zaɓar tumin dare.

Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin Nijeriyar da hankula zasu karkata musamman ganin irin yadda fagen siyasar jihar ke ƙara ɗaukar ɗumi.

Allah Ya Sa mu dace.

Daga MUSTAPHA MUSA, 08168716583.