Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rikicin da ke cikin Jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano na neman ƙazancewa, inda gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya fara ƙin daga wayar mai gidansa Rabi’u Musa Kwankwaso sannan ya ƙi halartar tarukan da jagoran NNPP din na ƙasa ya shirya.
Da alama dai wannan taken na “Abba tsaya da ƙafar ka” ya fara tasiri a gurin gwamnan bayan da wasu ke ta motsa yadda zai karɓe iko da jam’iyyar da kuma Kwankwasiyya daga hannun Kwankwaso.
Wasu majiyoyi sun shaidawa Manhaja cewa tuni Abba ya fara amsa kira bayan da “aka nusar da shi cewa Kwankwaso ne ke juya gwamnatinsa inda kusan kashi 90 na makaman da Abba ya yi daga ɓangaren Kwankwaso ne.”
Majiyoyi sun bayyana cewa Abba ba ya jin daɗin “ƙarfa-ƙarfa” da Kwankwaso ya ke yi masa inda ya ya fara nuna alamun boyewa masu kira da ya tsaya da kafar sa domin ci gaban sa na siyasa da ma jihar Kano baki ɗaya.
Tun lokacin da aka ga gwamnan a bikin murnar zagayowar haihuwar Kwankwaso, har yanzu ba su sake haɗuwa ba.
Majiyoyi sun bayyana wa Manhaja cewa duk tarukan da Kwankwaso ya kira a Kano da Abuja Abban bai halarta ba.
Majiyoyin sun ƙara da cewa har Abuja Kwankwaso ya bi gwamnan amma Abba bai bari sun haɗu ba, kuma har ɗan aike ya tura amma Abban ya ƙi ganuwa a wajen Kwankwaso.
Hakan na zuwa ne yayin da ‘yan majalisar wakilai biyu, Ali Madaki mai wakiltar Dala da Alhassan Rurum mai wakiltar Rano da Kibiya suka fice daga Kwankwasiyya a ranar Lahadi, wani lamari da ya ƙara fito da riƙon da ke cikin jam’iyyar.
“Yanzu haka ana shirin hada kai da wasu ‘yan APC da yan ƙungiyar Abba Tsaya da ƙafar ka wajen samo umarnin kotu da zai kori dukka waɗannan ciyamomin da aka rantsar sai a hana CBN da ma’aikatar kuɗi ta hana su kuɗin wata-wata sai dai a bai wa tsagin da Mai Shari’a Simon Amobeda ya tabbatar ana gobe zaɓe,” in ji majiyar.
Sai dai Manhaja ta gaza jin ta bakin Kwankwaso, amma wani na jikinsa ya nuna rashin jin daɗin halayyar da Abba ke nuna wa Kwankwason.
Shi ma mai magana da yaƙin Abba, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya ƙi cewa uffan akan batun.
Rikicin ya ci kujerar Sakataren dindindin, daraktoci a ofishin mataimakinsa da wasu
Rikicin da ke faruwa a Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya ɗauki sabon salo, yayin da Gwamna Abba Yusuf ya tura babban sakataren ayyuka na musamman Aminu Kura a ofishin mataimakin gwamna da kuma babban sakatare a ma’aikatar ƙananan hukumomi, Ibrahim Kabara.
Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam, ya riƙe matsayin kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar.
Yayin da aka tura Mista Kabara zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman ta ‘arid’, an tura Mista Kura zuwa ofishin shugaban ma’aikata, ba tare da wani fayil ba.
Don haka gwamnan ya amince da naɗin Sadi Ibrahim a matsayin sakatare na dindindin, ayyuka na musamman, ofishin mataimakin gwamna da Musbahu Badawi, sakatare na dindindin a ma’aikatar ƙananan hukumomi da masarautu.
Gwamnan ya kuma amince da naɗin Aminu Kabara da Jamilu Muhd daraktoci na albashi & Ma’aikata da ɗaukar ma’aikata da horaswa daga ma’aikatar ƙananan hukumomi zuwa ofishin shugaban ma’aikata don sake naɗa su.
Duk da cewa sabbin muƙaman sun bayyana, a fili, a matsayin wani sabon salo na ma’aikatan gwamnati da ya shafi ma’aikatu da cibiyoyi daban-daban da suka haɗa da gidan gwamnati, amma masu bincike sun alaƙanta korar manyan jami’an ofishin mataimakin gwamna da ma’aikatar ƙananan hukumomi da na baya-bayan nan da rikicin cikin jam’iyyar.
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne jaridar Manhaja ta ruwaito rikicin da ke kunno kai a jam’iyyar da kuma dangantakar ta sa soma yin tsami tsakanin gwamna da jagoran jam’iyyar na ƙasa, Rabi’u Kwankwaso.
Dangantakar gwamnan da mataimakinsa ta ƙara ja baya, biyo bayan wata badaƙalar sayen magunguna da kamfanin Novomed, mallakin Musa Garba Kwankwaso, wanda dan uwa ne ga shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Masu lura da al’amura dai na kallon matakin na gwamnan a matsayin hanyar gudanar da mulki na daƙile ikon mataimakin gwamnan kan harkokin ƙananan hukumomi.
A wata takarda mai ɗauke da kwanan watan Nuwamba 4, 2024 mai ɗauke da sa hannun sakataren dindindin na ofishin shugaban ma’aikata Umar Jalo, gwamnan ya sake nada sabbin sakatarorin dindindin da wasu daraktoci a ma’aikatar ƙananan hukumomi da kuma wasu ‘yan ma’aikatu.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa wannan jarida cewa ba a tuntuɓi mataimakin gwamnan ba kafin sabon muƙamin.
“Al’adar ita ce ofishin Mataimakin Gwamna yana zaɓar manyan ma’aikatan gwamnati a ofishinsa sannan ya tura su ga gwamna domin ya amince da kuma aika su. A cikin waɗannan sabbin muƙamai, ba a tuntuɓi mataimakin gwamnan ba.
“Wannan wata alama ce ta rashin jituwa tsakanin gwamnan da mataimakinsa,” in ji shi.
Sai dai wasu majiyoyi sun ce an aika da jami’an da abin ya shafa ne saboda tuhumar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta yi a kan badaƙalar Novomed.
Kakakin gwamnan, Sanusi Dawakin Tofa, ba a samu jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.