Rikici tsakanin ‘yan fim da ‘yan jarida a fim ɗin Labarina

Daga ABDUSSALAM BARISTA HOTORO

Wasu ‘yan jaridu sun koka kan yadda suka yi tunnain an ci zarfin ɗan jarida a cikin fim mai dogon zango mai suna Labarina. A cikin kashi na 11 a zango na uku an nuna ɗan jarida na neman ba’asi a wajen fitaccen mawaƙi Nazir M. Ahmad (Sarkin Waƙa) dangane da rayuwar Sumayya (Nafisa Abdullahi) wanda ya jaddada ita ya kamata a tuntuɓa kasancewar rayuwar ce.

A yayin da ɗan jarida ya dage wajen bibiyar labari sai Naziru ya nemi a ba wa ɗan jarida kuɗin mota don yayi na mota alamun ba zai iya samun amsar tambayar da yake nema daga gare shi ba.

Masu da’awar an wulaƙanta ɗan jarida a wannan shirin sun yi ta kiran lambar Daraktan fim ɗin, Malam Aminu Saira, don jin ta bakinsa, “Marubucin wannan shiri Nasir Gwangwazo tsohon ɗan jarida ne da ya ɗauki tsawon shekaru yana aikin jarida a babbar jaridar LEADERSHIP A YAU wanda har matsayin babban edita ya riƙe, kuma yanzu haka ma shi ne editan jaridar MANHAJA da kamfanin BLUEPRINT ke wallafawa.

Shin zai yi wani abu ne don muzanta aikinsa da yake cin abinci da shi? Ba mamaki ya san akwai ‘yan jarida da suke zubar da mutuncin aikinsu wajen yawon maula da roƙo shi ne ya rubuta hakan don jan hankalinsu a kan riƙe mutuncin kansu.

Ko a kwanakin baya an samu taƙaddama tsakanin ‘yan jaridu a jihar Kano inda wani babba daga cikinsu ya soki masu irin wannan hali na yi wa ‘yan siyasa maula da tumasanci. Kuma kamar yadda a kowane sashi na rayuwa akan iya samun nagari da na ƙwarai, suma ‘yan jaridu ba mala’iku ba ne da za a ce babu nagari da na banza a cikin su.

Kamfanin Saira Movies ne ya shirya fim ɗin Malika a shekarun baya da har gobe babu wani fim a masana’antar Kannywood da ya fito da kima da darajar aikin jarida sama da shi. An nuna babban jarumi da ake yi wa laƙabi da Sarkin Kannywood a matsayin ɗan jarida mai tsattsauran ra’ayi a kan kiyaye dokokin aikin jarida.

Fim ɗin da marubuci kuma ɗan jarida Maje El-Hajeej Hotoro ya rubuta shi ma babban ɗan jarida ne, wanda yake da gogewa a kan aikin jarida, shin ko sauran ‘yan jarida sun yi masa rubutun yabo a kan wannan gagarumin aiki?

Fim ɗin Malika ya yi tashe da shaharar da ya kamata ‘yan jaridu su yi kishin aikinsu wajen yaɗa shi ko yin rubutun yabo ga kamfanin a matsayin ƙarfafa gwiwa, amma babu wata rubutacciyar shaidar yin hakan sai yanzu suka ga an yi musu ba daidai ba.

Shin me ‘yan jarida suke so? Ba a ba wa wasu ‘yan jaridu na goro ne ko kuwa su ba sa ganin aikin alheri ne sai an taɓa su?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *