An samu rikici mai tsanani tsakanin masu addinin gargajiya da matasan Musulmi a garin Shimankar, ƙaramar hukumar Shendam, Jihar Filato, wanda ya jawo munanan raunika ga mutane da kuma asarar dukiya mai yawa.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne lokacin da masu addinin gargajiya suka bi ta cikin garin, inda aka samu hatsaniya tsakaninsu da wasu matasan Musulmi.
Rikicin ya ƙazanta sosai, inda aka kona gidaje, cibiyoyin addini, da kuma wuraren kasuwanci. Duk da isowar ‘yan sanda da sojoji cikin dare daga Lahadi zuwa safiyar Litinin, rigimar ta ci gaba da bazuwa, lamarin da ya sa al’umma suka tsere daga gidajensu domin neman tsira.
Mazauna garin, musamman mata da yara, sun yi gudun hijira domin tsira da rayukansu, yayin da aka rufe kasuwanni da sauran harkokin yau da kullum saboda rashin tsaro.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu akwai fargaba a cikin al’umma, duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na kwantar da tarzomar.
Har zuwa lokacin da ake tattara wannan rahoto, DSP Atebo Alfred, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, bai fitar da wata sanarwa ba game da lamarin. Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomi da su tura ƙarin jami’an tsaro don dawo da zaman lafiya tare da hana rikicin ƙara bazuwa.