Rikici ya ɓarke a wurin zaɓe a Bayelsa

An samu aukuwar rikici a wasu mazaɓu a yankin Ogbia, Jihar Bayelsa a wannan Aasabar da ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na’yan majalisun jihohi.

Manhaja ta tattaro cewar kayan zaɓen da aka tanada wa gundumar Ogbia ta 2, 3, 4 da ta 5 a Ƙaramar Hukumar Ogbia ta jihar, an lalata su sannan aka yi awon gaba da su.

Tuni Gwamnan Jihar, Douye Diri, ya yi tir da wannan ɗanyen aiki.

Gwmnan ya yi kira ga Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda nmda ma Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar da su maido da zaman lumana a yankin.