A matayin wani yunƙuri na neman kashe wutar rikicin jam’iyyar APC da ke ci gaba da ruruwa a jihar Kano, Gwamnan Yobe kuma shugaban riƙo na APC na ƙasa, Mai Mala Buni, ya sake ganawa da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau.
Ganawar wadda aka shafe kusan sa’o’i shida ana yin ta, ta gudana ne a masaukin gwamnan Yobe da ke birnin tarayya, Abuja.
Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna yayin zaman, kowane ɓangare ya gabatar da buƙatunsa tare da shawarwarin kan yadda za a shawo kan rashin jituwar da ke tsakani.
Majiyarmu ta ce Babban Ofishin APC da ke Abuja ya karɓi bayanan zaman sulhun da aka yi a Juma’ar da ta gabata da kuma buƙatun da duka ɓangarorin suka gabatar yayin zaman.
“Uwar jami’yyar ta ƙasa ta yi alƙawarin za ta nazarci duka buƙatun da aka gabatar a wajen zaman sannan ta ɗauki matsayar da za ta sanar da ɓangarorin yayin wani taro da za ta shirya nan gaba”, in ji majiyar.
Ko a ‘yan kwanakin baya masu ruwa da tsaki na APC sun yi wata ganawa kan rikicin in banda Gwamna Ganduje wanda wannan shi ne karonsa na farko na halartar taron.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da Yakubu Dogara da sauransu na daga cikin waɗanda suka mara wa Gwamna Buni baya yayin zaman sulhunta tsakanin tsagin Ganduje da na Shekarau.