Rikicin APC: Ganduje ya lallasa Shekarau a Kotun Ɗaukaka Ƙara

Daga BASHIR ISAH

A ranar Alhamis da ta gabata Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta shure hukuncin da Babbar Kotun Abuja ta yanke na rushe zaɓen shugabannin jam’iyyar APC a matakin unguwanni da ƙananan hukumomi da jihar Kano ta gudanar kwanan baya.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta yi na’am da duka ƙararraki guda ukun da ɓangaren Gwamna Ganduje ya ɗaukaka aa gabanta.

Jim kaɗan bayan kammala zaɓen APC na Kano, ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya shigar da ƙara gaban Babbar Kotun Abuja yana mai ƙalubalantar sahinhanci zaɓen tare da neman kotu ta rushe zaɓen sannan ta naɗa ‘yan ɓangarensa a matsayin halastattun shugabannin APC na jihar.

Sakamakon nasarar da tsagin Shekarau ya samu a ƙarar da ya shigar kotu ya sanya shi ma ɓangaren Ganduje ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙarar da ke Abuja, inda ya buƙaci kotun ta shure hukuncin da Babbar Kotun ta yanke sannan ta halasta zaɓen da aka gudanar.

Da take yanke hukuncinta, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce kotun da ta saurari ƙarar su Shekarau ba ta da hurumin yin haka.

Kazalika, ta ce matsalar, ba matsala ce ta gabanin zaɓe ba, face matsala ce ‘yar cikin gida wadda ya kamata a warware ta a gaban uwar jam’iyyar APC.

Da wannan nasarar da ɓangaren Ganduje ya samu a Kotun Ɗaukaka Ƙara, tuni ikon jujjuya jam’iyyar APC na Kano ya koma hannun Ganduje tare da Prince Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyya.

Da yake ganawa da manema labarai kan nasarar da suka samu, Ganduje ya yi kira ga Sanata Shekarau da mabiyansa da su bari a yi zaman lafiya da juna, sannan su zo su haɗa hannu da shi don ci gaba da gina jam’iyyar tasu yadda ya kamata, yana mai cewa Kano ta APC ce ɗari bisa ɗari.

Haka nan, Ganduje ya bada tabbacin ofishin APC na ƙasa ya tabbatar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano har ma ya miƙa masa satifiket.

Sanata Kabiru Gaya da Hon Ado Doguwa da dai sauransu, na daga cikin waɗanda suka yi wa Ganduje rakiya a wanann rana.