Rikicin APC ya ci kujerar Sakataren Jam’iyya na Ƙasa, Akpanudoedehe

Daga BASHIR ISAH

Da alama dai wutar rikicin da ta kunnu a cikin jam’iyyar APC mai mulki na ci gaba da ruruwa kamar wutar daji, lamarin da har ya kai ga sakataren APC na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe ya ajiye muƙaminsa.

Bayanan da Blueprint Manhaja ta kalato sun nuna cewa, Akpanudoedehe ya miƙa takardar ajiye muƙaminsa ne ga muƙaddashin shugaban riƙo na APC, Gwamna Abubakar Sani Bello yayin wani mitin da kwamitin riƙon ya saba gudanarwa a babbar sakatariyar jam’iyya a Abuja.

A ci gaba da bibiyar Blueprint Manhaja cikakken bayani na nan tafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *