Rikicin Bagudu da Aliero: Zaɓen ƙananan hukumomin Kebbi ya zamo ’yar manuniya

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Ranar Asabar 5 ga watan Fabrairun 2022 da ta gabata ne aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kebbi, sai dai zaɓen ya zama kamar ma’auni ne na farin jinin jam’iyyar APC mai mulki ko kuma na ɓangaren gwamnan jihar Sanata Atiku Bagudu.

Sai dai zaɓen ya bar baya da qura bayan bayyanar wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi Honarabul Aliyu Muhammed Mera, inda ta ke bayanin cewa an yi wa jam’iyyu goma sha takwas rajistar shiga zaɓen amma dai sha bakwai ne suka shiga takarar ɗaya ta kaurace da ake tsammanin jam’iyyar PRP ce da take kotu dangane da shari’a da hukumar zaɓen kan cancantar shugaban ta a matsayin sa na na ɗan jam’iyyar APC.
 
Takardar dai ta bayyana cewa an gudanar da zaɓen a mazaɓu 225 a cikin ƙananan hukumomi 21 da ke faɗin jihar kamar yadda dokar ƙasa ta bada hurumi, inda kuma jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun kansiloli da shugabannin ƙananan hukumomi.

Bayanai da suka mamaye kafafen sadarwa na zamani suna bayyana zaɓen dai yana cike da maguɗi inda har ta kai ga bai wa hammata iska a waɗansu wuraren da waɗansu manya da ke gudun jin kunyar faɗuwa a rumfunan mazaɓarsu.

Wani matashi a mazaɓar Nasarawa 2 Muhammed Nasiru inda kuma nan ne mazaɓar Maigirma Gwamna Atiku Bagudu, ya bayyana wa wakilinmu cewa duk da ya ke ba sa zaton adalci daga ɓangaren gwamnatin jihar Kebbi wajen wannan zaɓen, amma dai sun fito sun jefa ƙuri’a kuma sun fake amma kwatsam sai suka ji an sanar da wai APC ta lashe duk da an ƙirga PDP ce ta lashe wannan rumfar zaɓen.

Haka zalika a mazavar Nasarawa 1 jam’iyyar adawa ta PDP ita ce ta fi yawan ƙuri’u, inda nan ne mazaɓar Ministan Shari’a Abubakar Chika Malami.

Wakilinmu ya zanta da Alhaji Kabiru Muhammed Yakaji Dabai wani jagoran siyasa a yankin ƙasar Zuru inda ya bayyana cewa a wannan yankin na Zuru ba wani ɗan siyasa da ya je wani gari wajen yaqin neman zaɓe saboda kowa ya san da matsalar tsaro da ta addabi wannan yankin wanda saboda haka su kuma al’ummar wannan yankin suka zaɓi jam’iyyar PDP ƙwansu da ƙwarƙwata.

Bayan wannan kuma abin mamaki sai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi ta sanar da cewa wai APC ce ta lashe dukkan kujerun kansiloli da shugabannin ƙananan hukumomi na wannan yankin wanda wannan ba gaskiya ba ne.

Alhaji Isah Assalafi, jami’in hulɗa da jama’a na APC ɓangaren Gwamna Atiku Bagudu ya bayyanawa wakilinmu cewa an gudanar da zaven lafiya ƙalau kuma mutane sun fito sun zaɓi mutanen da su ke so su jagorance su a matakan ƙananan hukumomi.

Wannan zaɓen ƙananan hukumomin dai ya janyo kace-na-ce tsakanin al’ummar jihar Kebbi wanda har ya sanya masana da dama suka gabatar da sharhuna a kafafen yaɗa labarai na ciki da wajen jihar, inda su ke Allah wadai da irin wannan aikin a cikin dimokuraɗiyya.

Zaɓen dai ya zo ne daidai lokacin da dangatakar siyasa ta yi tsami tsakanin ɓangarori biyu na masu ƙarfin faɗa a ji a jihar da suka haɗa da ɓangaren Sanata Adamu Aliero jagoran siyasar jihar da kuma ɓangaren Gwamna Atiku Bagudu, inda ɓangaren Sanata Adamu Aliero ya tsaya kai da fata sai an ɗabbaƙa adalci a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar ta APC wajen rabon muqaman siyasa a daina shiga wani ɗaki ana rubuta sunayen mutanen da ake so saboda ana riƙe da madafun iko ba.

Wannan zaɓen dai ana ɗaukar sa ne a matsayin ‘yar manuniyar auna karɓuwar jam’iyyar APC ta ɓangaren Gwamna Atiku Bagudu da kuma ɗaya ɓangaren na Sanata Adamu Aliero. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *