Rikicin Biliri: Gwamanati ta kafa dokar hana zirga-zirga

Daga WAKILIN MU

Gwamnatin Jihar Gombe ta kafa dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 a garin Biliri da ke cikin ƙaramar hukmar Biliri, biyo bayan rikici da ya ɓarke a yankin.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahin Abubakar Njodi, ya fitar a Juma’ar da ta gabata, ta nuna dokar ta soma aiki kai tsaye ba tare da wani jinkiri ba da zummar maido da lumana a yankin da rikicin ya shafa.

“Gwamnatin jihar ta jaddada buƙatar zama da juna lafiya da kuma ƙoƙarinta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Saboda haka gwamnati ta dakatar da haɗa kowane nau’i na taro a yankin ƙaramar hukumar Biliri.

“An umarci duka hukumomin tsaro su kiyaye tare da tabbatar da jama’a sun yi biyayya ga wannan doka.

“An umarci duka ‘yan jihar su kiyaye wannan umarni in ban da ma’aikatan ayyuka na musamman”, inji sanarwar.