Rikicin Boko Haram ya yi ajalin mutum 35,000 a Arewa maso Gabas – MƊD

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta ce kimanin mutum 35,000 ne suka mutu tun fara rikicin Boko Haram daga shekara ta 2009 zuwa watan Agustan 2023.

Shugaban ofishin hukumar a Jihar Adamawa, Elsie Mills-Tetty ce ta bayyana hakan yayin wani taron horar da sojoji a kan kare haƙƙin bil Adama da kuma kare fararen hula a Yola ranar Laraba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa hukumar ta shirya taron ne domin ba su horo kan hanyoyin kiyaye haqqoqin jama’a yayin ayyukansu.

Elsie, wacce wani jami’i a hukumar, Umar Abdullahi ya wakilta, ta ce sun tattara alƙaluman ne daga rahoton wata cibiyar ƙasa da ƙasa mai suna GCRP na watan Agustan 2023.

Ta ce illar da rikicin ya yi wa harkokin tattalin arziki da na zamantakewar mazauna jihohin Borno da Yobe da Adamawa da ma Nijeriya baki ɗaya, ba za ta misaltu ba.

Jami’ar ta ce a shekara ta 2022, wani binciken hukumar ya bayar da rahoton take haƙƙin bil Adama da kuma hanyoyin magance su.