Rikicin Kasuwa: Gwamnonin sun ziyarci Shasha

Daga WAKILIN MU

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu, ya ce Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta yinƙura domin mara wa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo baya wajen dawo da zaman lafiya a kasuwar Shasha da ke Ibadan, bayan hargitsin da ya auku a kasuwar cikin makon da ya gabata.

Bagudu ya faɗi haka ne a Talatar da ta gabata, sa’ilin da yake magana da manema labarai yayin ziyarar gani da ido da shi da wasu takwararorinsa suka kai kasuwar.

Tawagar gwamnonin da ta yi wannan ziyara ta ƙunshi Gwamna Bagudu na jihar Kebbi da Abdulahi Ganduje na jihar Kano da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da Abubakar Sanni Bello na jihar Neja, sai kuma Gwamna Makinde na Oyo da ya kasance mai karɓar baƙi.

Bagudu ya ce za a bada tallafin kuɗin da ba a faɗi adadinsa ba ga waɗanda rikicin ya shafa, haka ma ƙarin tallafin zai biyo baya bayan sun gabatar da batun ga sauran mambobinsu na NGF

Ta bakin Bagudu, “Yanzu dai an rufe kasuwar wanda hakan ya shafi harkokin jama’a da daman gaske. Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya za ta goya wa Makinde baya wajen ganin cewa an taimaka wa waɗanda suka tafka hasara a rikicin.”

Ya ƙara da cewa bincikensu ya gano batun shugabanci tsakanin Hausawa da Yarabawa a kasuwar na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa rikincin.

A nasa ɓangaren, da yake yi wa ‘yan kasuwar bayani, Gwamna Makinde ya ce takwarorinsa daga Arewa sun ziyarci Baale na Shasha da Sarkin Shasha duka dai da zimmar lalubo mafita dangane da wannan rikici da ya auku.