Rikicin manoma da makiya ya ɗaiɗaita al’amura a Ƙaramar Hukumar Guri

Daga UMAR AKILU MAJERI  a Dutse

Rikicin manoma da makiyaya ya yi sanadin mutuwar mutane tara a yankin Ƙaramar Hukumar Guri da ke Jihar Jigawa a arewacin Nijeriya.

Rikicin da ya ɗauki tsawon kwanaki uku ana yi a yankin ya yi sanadin kashe Fulani shida da manoma uku, wasu a gonaki wasu a daji wajen da suke kiwon shanu. 

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ASP Lawan Shisu Adam ya tabbatar da cewar ‘yan sanda sun kama mutum goma da ake zargi da hannu dumu-dumu akan rikicin, kuma yanzu haka mutane uku suna asibitin Haɗeja suna karɓar kulawa.

Ya kuma ƙaryata labarin cewar mutane tara ne suka mutu, inda ya ce su a saninsu mutum ɗaya ne ya mutu mai suna Garba Ɗanladi wanda aka dake shi da sanda a tsakiyar kansa kuma tsinci gawarsa a dajin Gwam dake ƙauyen Dawa a yankin Ƙaramar Hukumar ta Guri.

Ya ci gaba da cewar da zarar sun kammala bincike akan waɗanda suke zargin za su gabatar da su a gaban shari’a domin kowa daga cikinsu ya girbi abinda ya shuka.

Wani mazaunin yankin kuma kwamandan Hisbah na yankin Malam Umar Iguda Guri ya ce a nasu binciken mutane uku daga ɓangaren manoma suka mutu, yayin da kuma a ɓangaren Fulani suka samu labarin mutuwar mutane huɗu.

Ya kuma tabbatar da cewar manoma sun tafka babbar asara ta kayan amfanin gona saboda Fulanin sun sanya dabbobi a gonakin sun cinye masu kayan amfani.

Ya ce gonakin shinkafa, masara da alkama sama da gonaki dubu ne makiyayan suka lalata wadda ya sa aka samu asarar kayan gona ta miliyoyin naira a yankin.

Ya ce sakamakon zuwan jami’an tsaro yanzu zaman lafiya ya fara dawowa a yankin, amma duk da haka ana nan ana zaman ɗarɗar ana hararar juna; Fulani ba sa zuwa gari yawo, matansu ba sa zuwa tallan nono, kuma manoma ba su da ikon zuwa gona, harkoki sun yi tsayuwar gauraka a yankin.

Sakamakon rikicin ya janwo an rufe ɗaukacin makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya dake yankin ƙaramar saboda mafiya yawan malaman Hausawa ne ba sa iya zuwa aiki saboda gudun kada rikicin ya ritsa da su.

Wata majiya mai tushe da ta buƙaci a sakaya sunanta ta ce Fulanin da suka haddasa rikicin ba ainihin mazauna yankin na Guri ba ne, baƙin Fulani ne matafiya da suka zo yankin suke yin kiwo kuma su ne suke haifar da rikici a yankin tsawon shekaru masu yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *