Daga IBRAHIM SHEME
An Buƙaci na fassarar rubutun da na yi kan saƙon da na tura wa wani aboki na yau da safe a hirar mu ta WhatsApp:
1. Kotun ɗaukaka ƙara ba ta sauke Malam Muhammadu Sanusi II ba, ta soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yi a kan sa ne. Saboda haka har yanzu dai yana nan a matsayin Sarkin Kano.
2. Abin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi kawai shi ne ta umarci Babbar Kotun jiha da ta sake naɗa wani alƙalin wanda zai yi tushin shari’ar.
A zahiri, Gwamnatin Jihar Kano ce ke da iko kan wannan kotun. To, ya ka ke ganin hukuncin da za ta zartas zai kasance? Saboda haka, duk ta inda ka kalli lamarin, hukuncin da kotu ta yanke jiya ya fi yi wa Sanusi daɗi fiye da Alhaji Aminu Ado Bayero.
Farfagandar son rai ce da wasu ke yaɗawa cewa wai hukuncin ya yi wa Aminu daidai, ga shi kuma ba mu ga Aminun yana murnar hukuncin a gidan sa na Nassarawa ba kamar yadda ɓangaren su Sanusi suka yi.
Har bidiyo Sanusi ya saki daga ƙofar Kudu yana gode wa Allah Maɗaukakin Sarki kan nasarar da ya samu tare da roƙon magoya bayan sa da su kwantar da hankalin su. Shin ka ga ɗaya ɓangaren suna irin wannan murnar ne?
A gani na, babu wata kotu da za ta tuɓe Malam Sanusi. Wata gwamnatin kaɗai ce za ta iya sauke shi idan har hakan zai iya yiwuwa wata rana. Saboda haka, duk waɗannan kes-kes da ake yi a kotu, kawai ana yawo da hankalin jama’a ne bisa son rai wanda a ƙarshe ana ruɗar da mabiyan su, ana gwara kan ‘yan soshiyal midiya, sannan ana azurta lauyoyi da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin yayin da mu kuma ake ɓata mana lokaci da kuɗin data.
Idan kun tuna, sarakuna daga kan na Gwandu (Jokolo) zuwa na Sokoto (Dasuƙi) zuwa na Muri (Tukur) zuwa na Kano (Sanusi I da Sanusi II), ds, ba kotu ce ta tsige su ba, a’a shugabannin siyasa ne na mulkin soja ko farar hula.
Daga cikin su, wasu sun nemi haƙƙin su a kotu domin a mayar da su kan karagar su, to amma sun ɓata wa kan su lokaci da dukiya ne kawai domin kotunan ba su taimake su ba. Ai a 2024 ba kotu ce ta dawo da Sanusi II ba, gwamna ne ya rattaba hannu a takarda tare da ambaton wasu kalmomin kundin shari’a. Ko a zamanin mulkin mallaka, shugaban jiha, wanda ake kira Razdan, shi ne yake naɗa ko cire sarki ko hakimi, ba wata kotu ba.
Ni a hangen da na yi, in ban da kes ɗin Sarkin Suleja Malam Awwal Ibrahim, wanda ba a saba ganin irin shi ba, kotu ba ta da wani ƙarfi a maganar naɗa sarakuna; magen Lami ce kawai. In da a ce ni sarki ne sai gwamna ya tuɓe ni, to kawai tafiya ta zan yi kamar yadda Sarkin Bichi ya yi, ba zan ja wa kai na hawan jini a ƙoƙarin sai na ƙwato karagar ba.
Ba zan yarda in zama kurar wasan wasu ba waɗanda za su riƙa amfani da ni domin cimma wata manufa tasu ta ƙashin kan su.
Ibrahim Sheme, wanda ɗan jarida ne a Abuja, ya wallafa ne a shafinsa na Facebook