Rikicin PDP: kotu a Kano ta yi fatali da karar Aminu Wali

Wata kotun gwamnatin tarayya a Kano, tayi watsi da karar da tsagin jam’iyyar karkashin jagorancin Alhaji Aminu Wali ya shigar, in da ya nemi kotun ta hana tsagin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shirya zaben shugabannin Jam’iyyar daga matakin kananan hukumomi zuwa na jiha.

Dama dai akwai wata jikakka a tsakanin bangarorin guda biyu, tun bayan da tsohon gwamnan ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC ya komo PDP.

Jaridar Manhaja ta tuntubi lauyan na tsagin kwankwasiya, Lauya Bashir Yusuf, domin yayi mata karin haske akan yadda karar ta kasance ” Tun farko dai su tsagin da suka shigar da kara, suna neman kotu da ta hana tsagin kwankwasiyya shirya zaben shugabanni ne, daga matakin kananan hukumomi zuwa na jiha. Amma mun gabatarwa da kotu hujjoji kwarara da suke nuna, wannan kara bata da wata kwakkwarar hujja da za a karbe ta, haka kuma masu karar ba su da hurumin zuwa”

Lauyan ya kara da cewa ” a kaida ta jam’iyya baka zuwa kotu, har sai bayan ka gabatar wa da jam’iyya korafinka, haka kuma shigar da karar ya saba wa dokar shigar da karar zabe, domin an haura lokacin da mai korafi zai iya kai kara. Bisa ga wadannan kwararan dalilai ne, ya sanya kotu ta amince da korar karar”

Jaridar Manhaja ta yi kokarin tuntubar tsagin na ambasada Aminu Wali, akan ko za su karbi kaddara su amince da hukuncin kotu, ko kuma za su daukaka kara, amma dai bamu samu wanda zai mana bayani ba.

A yanzu dai kamar yadda mai magana da yawun Kwankwasiyyar ya sanar mana, za su cigaba da shirye shiryen fara zabukan na shugabanni da sauran yan kwamitin zartaswa na jam’iyyar a matakin kananan hukumomi da jihohi.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*