Rikicin siyasa ya ci ran mutum ɗaya a Kazaure

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Mutum ɗaya ya riga mu gidan gaske sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan Jam’iyyar APC taron siyasar da jam’iyyar ta shirya garin Kazaure.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa, Emmanuel Ekot, ya raba wa manena labarai ranar Laraba, ya ce mutum ɗaya ya rasa ransa ne sakamakon sa-in-sa da ɗaya daga cikin abokan tafiyarsa.

Jami’in ya ƙara da cewa tuni wanda ake zargi ya tsere zuwa Jihar Kano inda yanzu haka suka baza komarsu domin damƙo shi a gurfanar da shi gaban shari’a.

Wani bincike ya nuna marigayin mai suna Halilu Lafka, magoyin bayan ɗan takarar sanata na Jigawa ta Yamma, Alhaji Babangida Hussaini ne.

Kisan ya sa fusatattun matasa a yankin bi suna cire hotunan ɗan takarar sanatan da aka lilliƙa a wurare daban-daban a ƙwaryar Kazaure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *