Rikicin Sudan: An kashe fitacciyar mawaƙiya Shaden Gardood

Daga AISHA ASAS

An kashe ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Sudan Shaden Gardood, a wata musayar wuta tsakanin ɓangarori biyun da ke faɗa da juna a ƙasar.

Misis Gardood ta rasa ranta ranar Juma’a a birnin Omdurman sakamakon faɗa tsakanin sojojin qasar da dakarun RSF.

Mutuwar mawaƙiyar mai shekara 37 na zuwa ne kwana guda bayan ɓangarorin da ke rikici da juna sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen wahalar da fararen hula ke fuskanta.

Gardood dai na zaune ne a al-Hashmab, inda dakarun RSF ke ƙaruwa a ‘yan kwanakin nan.

Wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta an ga Gardoon na ɓuya tare da kiran ɗanta ya matsa daga kusa da taga domin kauce wa harsasai, yayin da ake ci gaba da luguden wuta a birnin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *