Rikicin Sudan: Babu halin kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a ƙasa a halin yanzu – Gwamnati

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwarta kan rashin iya kwaso ‘yan ƙasar da suka maƙale a Ƙasar Sudan mai fama da rikici.

Ta ce yanayi da kuma haɗarin da ke tattare da hakan ya hana kowane jirgi tashi a halin yanzu.

Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Nijeriya Mazauna Ƙetare, (NiDCOM), Hon Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana hakan.

Ta ce Nijeriya tare da haɗin gwiwar Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun kammala tsare-tsare don maido da ɗaliban Nijeriya da sauransu da suka maƙale a Ƙasar Sudan.

A cewarta, da safiyar ranar Alhamis aka ƙona jiragen saman da ke filin jirgin saman Sudan sakamakon rikicin da ƙasar ke fama da shi.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na NIDCOM, Gabriel Odu, ya rattaɓa hannu ranar Juma’a.

Dabiri-Erewa ta ƙara da cewa, ƙungiyoyin jinƙai na ci gaba da ƙoƙarin lalubo hanyoyin isar da abinci da magunguna ga waɗanda lamarin ya shafa a ƙasar ta Sudan.

Daga nan, ta nemi ɓangarorin da rikicin ya shafa da su yi haƙuri su rungumi yarjejeniyar zaman lafiya ta hukumar cigaban ƙasashen duniya (IGAD), a matsayin matakin samar da zaman lumana a ƙasar.

Tuni Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa Arewa (AYCF), ta bakin shugabanta na ƙasa, Yarima Shettima, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya a kan ta yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da ta kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a Sudan ba tare da ɓata lokaci ba.