Rikicin Sudan: Maƙalallun ‘yan Nijeriya 350 na hanyar dawowa gida daga Masar bayan nasarar kwashe su daga Sudan

An sake samun nasarar kwashe wani rukuni na ‘yan Nijeriya da suka maƙale a Sudan zuwa ƙasar Masar a ranar Laraba.

Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙetare (NiDCOM), ta tabbatar da hakan a shafinta na Tiwita, inda ta ce ‘yan Nijeriyar sun isa Masar daga Sudan lafiya ƙalau, yanzu kuma suna shirin barin Masar zuwa Nijeriya.

“Fasinjoji 350 sun isa Filin Jirgin Saman Aswan da misalin ƙarfe 9.30 am. Jirgin saman NAF C130 ne zai kwashe su” zuwa gida Nijeriya, in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa, jirgi mai lamba “C130 zai kwashi fasinja 80, yayin da Airpeace zai ɗebi fasinja 274.

Kuma tuni sun fara shiga jirgin bisa tsarin dokokin filin jirgi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *