Rikicin Yukren: Rasha ta amince da amsar Bitkoyin a matsayin kuɗin cinikin gas

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙasar Rasha ta ba da dama ga masu sayen gas a wajenta da za su iya biya da kuɗaɗen ƙasar da suka ga dama ko ma bitkoyin. Shugaban kwamitin ƙasar Rasha a kan harkar makamashi shi ya bayyana haka. Amma fa ba kowacce ƙasa za a iya yin wannan ciniki da ita ba, sai ƙasashen da suke ‘ɗasawa’ da ƙasar ta Rasha. 

Mujallar Ingilishi wacce take labarai a kan Bitkoyin, Namcios  Bitcoin Magazine ta rawaito cewa, Shugaban Kwamitin na makamashi a ƙasar Rasha mai suna Pavel Zavalny, ya bayyana cewa, ƙasar Rasha za ta fara amsar Bitkoyin a matsayin kuɗin gas a yayin zantawarsa da ‘yan jaridu a taron manema labarai na ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata.

Zavalny  ya ƙara da cewa: Hakazalika, ƙofar Rasha a buɗe take don amsar kuɗin kowacce ƙasa ne don yin safarar kaya daga ƙasar, tun daga kan gas har komai ma. A cewar sa ya danganta da ra’ayin mai sayen kayan. Sannan kuma sharuɗɗan cinikayya ta danganta ne da iri alaƙa mai kyau ko mara kyau dake tsakanin Rasha da ƙasar da za a yi cinikin da ita. 

A cewar Pavel Zavalny, “Idan ana maganar ƙawayenmu kamar ƙasashen Chana da Turkey waɗanda ba sa takura mana, su mun jima muna sayar musu da kaya su biya mu da kuɗaɗensu ‘rubles da yuan”. Inji shi.

“Amma ita kuma Turkey za mu iya sayar mata ta biya mu da lira da rubles. Don haka akwai nau’in kuɗaɗe daban-daban. Wannan shi ne tsari da sharaɗin cinikayya. Kuma idan ma Bitkoyin ne da su, sai mu yi cinikin da Bitkoyin”.

Wannan sanarwar ta Zavalny ta zo ne kwamaki kaɗan bayan  shugaba Vladimir Putin na ƙasar ta Rasha ya ba da sanarwar tilas ƙasashen da ba sa ɗasawa da Rashan tilas su biya da ‘Rubles’ in dai har suma son sayen gas a hannunta. Sai dai tabbas mutane sun fahimci saƙon na Putin.

Amma abinda har yanzu suke cikin duhu a kai shi ne, yaya ƙasar Rashar za ta yi da kwangiloli da cinikayyarta da ta ƙulla da wasu ƙasashen a kan Yuro?

A wani taro da kwamitin ƙasar Rasha kan makamashi suka gudanar, sun yi ƙari a kan hukuncin da Putin ɗin ya yanke. Inda suke ganin ya kamata Rasha ta sa zinare/gwal a cikin kuɗaɗen da za ta dinga amsa a lokacin cinikin gas ɗin. 

“Idan har za mu yi ciniki da ƙasashen yamma (Turai da Amurka) dole ne su biya da dukiya mai ciwo, wacce ita ce Zinare. Ko kuma su biya da nau’in kuɗin da ya fi mana kwanciyar rai. Wato kuɗinmu na ƙasa, ‘Ruble’. Wannan amma ya shafi ƙasashe maƙiyanmu ne kawai”. Inji Zavalny.

Shugaba Putin ya bayyana cewa, da ma can ya san akwai Bitkoyin, kuma sannan ya san yana da daraja. Amma bai taɓa zaton akwai wani lokaci da za a yi amfani da shi wajen cinikayyar Fetur da gas ba. 

Shi dai Bitkoyin wasu sulalla ne da ake hada-hadarsu ta yanar gizo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *