Rodger Federer ya yi ritaya daga wasan Tennis

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Fitaccen ɗan wasan tennis ɗan ƙasar Switzerland, Roger Federer ya sanar da yin ritaya daga fagen wasan Tennis bayan da ya lashe kofuna sama da 103, da manyan wasanni 20 a cikin shekaru ashirin da huɗu na ganiyarsa a wasan ƙwallon Tennis.

Federer ya fitar da sanarwa a shafinsa na Tiwuta, “wasan cin kofin Laver da za a yi a mako mai zuwa a Landan zai zama taron ATP na ƙarshe”.

Ɗan wasan mai shekaru 41, wanda ya lashe kofunan Grand Slam 20 bai taka leda ba tun bayan da ya yi rashin nasara a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a Wimbledon a shekarar 2021, bayan da aka yi masa tiyatar gwiwa ta uku a cikin watanni 18.

Shahararriyar ‘yar wasan Tennis Serena Williams ita ma ta rataye takalminta, bayan ficewarta a gasar US Open a zagaye na uku a wannan watan.

Federer ya ce, jikinsa ya gaya masa cewa lokaci ya yi da ya kamata ya rataye takalmansa.

“Na yi aiki tuƙuru don ganin na cimma burika a wannan fagen wasa,“ a cewar Federer.

“Amma ni kuma na san iyawa da yanayin jikina, kuma saƙonsa zuwa gare ni a kwanan nan ya fito fili.

“Ina da shekara 41. Na buga wasanni sama da 1500 sama da shekaru 24 kenan.

“Tennis ya ba ni kyauta fiye da yadda na ke mafarki, kuma yanzu dole ne in gane cewa lokaci da ya kamata na dakata,” inji shi.