Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Roma ta kammala ƙulla yarjejeniyar karɓar aron Romelu Lukaku daga Chelsea wanda zai shafe tsawon kakar bana ya na takawa ƙungiyar mai doka gasar Serie A leda.
Roma ƙarƙashin jagorancin Jose Mourinho ta bi sahun manyan ƙungiyoyin Turai da suka miƙa buƙatar karvar aron Lukaku ne bayan da Mauricio Pochettino ya bayyana cewa ɗan wasan baya sahun waɗanda zai yi amfani da su a wannan kaka.
Lukaku ɗan Belgium mai shekaru 30 da kanshi ya zabi komawa Roma fiye da Inter Milan ƙungiyar da ya kai wasan ƙarshe na gasar kofin zakarun Turai a bara, amma kuma suka yi rashin nasara a hannun Manchester City.
Wasu rahotanni sun ce gabanin komawa Roma a ranar Alhamis, kungiyoyin Lig ɗin Saudiya da dama sun tuntuvi ɗan wasan na Belgium amma ya yi watsi da tayinsu.
Tuni dai Lukaku ya isa Roma inda ya samu tarba ta musamman daga dubunnan magoya bayan ƙungiyar da suka yi dafifin tarbar shi.
A jawabin da ya gabatar, Lukaku ya ce tarba da ƙaunar da ƙungiyar ta Roma ta nuna masa zai ƙara masa ƙwarin gwiwar bayar da gagarumar gudunmawa.