Ronaldo ya kafa sabon tarihi a duniyar ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kyaftin ɗin Portugal Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihin zama ɗan wasa na farko da ya buga wasannin ƙasa da ƙasa 200 a wasan neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Turai ta Euro 2024 da suka doke Iceland da ci 1-0.

Ɗan wasan mai shekaru 38 shine ya ci ƙwallon da ta bai wa Purtgal nasara a mintuna na 89 ana daf da ƙarƙare wasa.

Da farko alƙali ya zaci ƙwallon satar fage ce, amma na’urar VAR ya amince da cin lamarin da ya faranta wa Ronaldo a daren mai cike da tarihi.

Wannan ita ce ƙwallo ta 123 da Ronaldo ya ci a wasannin ƙasa da ƙasa na duniya, wanda ya ƙara tarihinsa a duniya.

Ronaldo na Al-Nassr ya karya tarihin ɗan wasan Kuwait Bader Al-Mutawa da cika wasanni 196 a cikin watan Maris ɗin da ya gabata, kuma tuni Guinness World Records suka miƙa masa shaidar yabo tun kafin fara wasa.

Tsohon ɗan wasan Sporting Lisbon, Manchester United, Real Madrid da Juventus ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar.

Ƙwallon da ya ci ta biyar a wasan neman tikitin shiga gasar Euro 2024 ya taimaka wa Portugal da ci huɗu a wasanni huɗu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *