Ronaldo ya yi fatan Morocco ta ɗauki Kofin Duniya na 2022

Dag BASHIR ISAH

Fitaccen ɗan ƙwallon ƙafar nan na ƙasar Brazil, Ronaldo Nazario de Lima, ya yi fatan ƙasar Morocco ta lashe Gasar Kofin Duniya da ke gudana a Qatar.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Morocco, Atlas Lions ce ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta taɓa kaiwa matakin na kusa da ƙarshe a tarihin gasar.

Morocco ta taki wannan nasarar ce bayan da ta lallasa Portugal da ci ɗaya da nema (1-0) a fafatawar da suka yi a Filin Wasannin Motsa Jiki na Al Thumama da ke Doha.

Duk da an yi waje da ƙasarsa Brazil a gasarsa, Ronaldo ya nuna goyon bayansa ga Morocco tare da fatan ita ce za ta ɗauki Kofin Duniyar.

“Ina son su (‘yan wasan Morocco) ɗauki Kofin Duniya. Komai nasu ya zamanto da armashi. Yadda suke kai kora da kare gidansu da yadda suka haɗe kansu,” in ji Ronaldo.