Ronaldo ya zaɓi mawaƙin da ya fi so tsakanin Wizkid da Davido

Daga BELLO A. BABAJI

Zakaran ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo ya zaɓi mawaƙin da ya fi so’ tsakanin Davido da Wizkid, waɗanda su biyun ƴan Najeriya ne.

Tsohon ɗan wasan ƙungiyar Real Madrid ɗin yayin wallafa wani shiri a shafinsa na YouTube a ranar 29 ga watan Oktoba, 2024, ya samu zaɓin ɗaukar ɗaya daga cikin mawaƙan.

Yayin ɗaukar wanda ya fi so, Ronaldo ya zaɓi Davido akan Wizkid.

Hakan na zuwa ne yayin da ake gwabza hamayya tsakanin mawaƙan Najeriya.

A baya ne Blueprint ta ruwaito inda Ronaldo ya jinjina wa waƙar Asake, wanda a ciki ya haska wani mawaƙin Amurka mai suna Travis Scott.