RTEAN ta naɗa shugaban riƙo na Legas

Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri ta Nijeriya, RTEAN, ta naɗa Areshola Kudus a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na RTEAN na Jihar Legas.

Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa, Comared Yusuf Ibrahim Adeniyi

Mataimakin Shugaban RTEAN na uku na shiyyar Kudu maso Yamma, Barista Samuel Olugbenga Agbede, ya shaida wa manema labarai cewa an cimma matsayar naɗa Kudus a wannan matsayin yain taron da shugabancin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Dr. Musa Muhammed Maitakobi ya gudanar a ranar 24 ga Mayu, 2023 ya gudanar a RTEAN House.

Sanarwar ta ce naɗin ya yi daidai da tanadin Sashi na 7: 2ii(a) na kundi tsarin mulkin RTEAN.

Kazalika, sanarwar ta yi waiwaye kan yadda a bara Gwamnatin Jihar Legas ta rushe shugabancin RTEAN a jihar, lamarin da ya sanya ƙungiyar garzayawa kotu domin kwato ‘yancinta.

Shugaban RTEAN na ƙasa, Muhammed Maitakobi, ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga mambobin ƙungiyar da su zamo masu bin doka da oda a kowane lokaci kuma a ko’ina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *