Ruɗani kan shigo da gurɓataccen fetur a Nijeriya

A Nijeriya masu ababan hawa sun shiga tsaka mai wuya sakamakon ƙarancin man fetur a gidajen mai da kuma samun gurɓataccen man da wasu ke sayarwa, abin da ya sa kasuwar bayan fage tashi.

Ruɗani a kan shigo da gurɓataccen man fetur ɗin dai ya jefa ’yan Nijeriya a hali na rashin tabbas a kan man da aka kwashe makwanni ana fuskantar ƙarancinsa, wanda dama aka danganta da alamu na sake fuskantar ƙari.

A ranar Talata ne sabuwar Hukumar kula da harkokin Sarrafa man fetur da tacewa da sufuri ta Nijeriya wato ‘Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority’ ta tabbatar da samun gurvataccen man ɗauke da wani adadin sinadarin ‘methanol’ da ya zarce abin da ƙasar ta iyakance a kasuwa.

Kafofin yaɗa labaran Nijeriya sun ambato ƙaramin ministan fetur jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwar ƙasar na cewa gwamnati ta tashi haiƙan wajen tunkarar batun gurɓataccen man fetur ɗin da ya cika gidajen mai.

Ministan ya kuma nemi ’yan ƙasar su ƙara haƙuri har gwamnati ta kammala bincike kafin a fara batun bayyana sunayen masu hannu.

Rahotanni sun kuma ambato shi yana cewa kafin yanzu babu wanda ke duba adadin ‘methanol’ a cikin man fetur ɗin da ake shiga da shi ƙasar.

Lamarin da ya sa wasu ke tambayar da ma ƙasar ba ta da sashen tantance ingancin man da ake shigarwa daga waje.

Jihohin Nijeriya da dama sun shiga wannan makon da matsananciyar matsalar man fetur, wadda daman tun bayan sati biyu da suka gabata ƙasar ke cikin wannan matsala.

Bayan kwanaki da fara fuskantar ƙarancin man sai kuma aka fara samun wani gurɓataccen man fetur wanda ya ringa lalata abubuwan hawa.

A dalilin samun wannan matsala hukumomi suka bayar da umarnin dakatar da sayar da man, har ma shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin cewa lallai sai waɗanda suka shigar da man ƙasar sun yi bayani, yana mai bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare ’yan ƙasar daga duk wani abu da za a samar wanda zai cutar da su.

Wannan matsala ta ƙarancin man dai ana ganin ta haifar da gagarumin koma-baya ga harkokin tattalin arzki na jama’a da ma gwamnati kuma za ta ci gaba da hakan har zuwa lokacin da za a shawo kanta.

Jama’a sun wayi gari a ranar Litinin ɗin nan 14 ga watan Fabrairu 2022, cikin tsananin wahalar man fetur ɗin fiye da sauran kwanakin da suka gabata, inda wasu gidajen mai suka kasance a rufe, ’yan kaɗan ɗin da suke sayarwa kuma wasu suka ƙara farashi a wasu jihohin Nijeriya.

A Abuja babban birnin tarayyar ƙasar, sakamakon ƙarancin man kasancewar wasu gidajen man ba sa sayarwa, ma’aikata da sauran jama’a sun gamu da tsananin wahala ta neman ababan hawan da za su kai su wuraren aiki da sauran hada-hada ta yau da kullum.

Hakan ne ya sa ababan hawan da ake da su suka yi ƙaranci matuƙa, abin da ya sa aka samu ƙarin farashi na zirga-zirga musamman a cikin birnin na Abuja.

Wasu ma’aikata da sauran jama’a kuwa sun riƙa takawa da ƙafa zuwa wuraren ayyukansu, inda ya kasance babu nisa sosai, amma ga waɗanda wurarensu ke da nisa sai dai su haƙura bayan shafe sa’o’i da dama ba su samu abun hawa ba.

Abin jira a gani dai shi ne ko bincike zai gudana kuma ya yi wani tasiri, ko kuma zai kasance irin bincike-binciken babarodo da aka saba yi a Nijeriya.

A baya-bayan nan an ambato ministar kuɗi Zainab Shamsuna na cewa ƙasar za ta kashe kimanin naira tirliyan talatin a matsayin tallafin man fetur a bana.

A wani mataki na tsaftace harkar man fetur dai, tun farkon mulkinsa, Shugaba Muhammadu Buhari ne da kansa, ke jagorantar sashen a matsayin babban ministan man fetur.
Gwamnoni da ’yan majalisa a bainar jama’a sun fito suna nuna shakku kan maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa a matsayin tallafin man fetur.

Wannan na nuna cewa mai yiwuwa ko a hukumance baki bai zo ɗaya ba, saboda yawan rufa-rufa da rashin fayyace komai a faifai da ake zargin sun cika harkar.

Da alamun ruɗanin da wannan lamari ya haifar zai ci gaba da tasiri a kan hada-hadar man fetur a Nijeriya, abin kuma da zai ci gaba da shafar rayuwar al’umma musamman ma marasa ƙarfi, wanda a da Nijeriya ta fi kowacce ƙasa ƙarfin arzikin man a nahiyar Afirka, kuma ta shida a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *