Ruɗani yayin da zaɓen ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa ya samar da shugabanni biyu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An samu ruɗani yayin da babban zaɓen da Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS) ta gudanar ya fitar da ’yan takara daban-daban guda biyu a matsayin shugaban ƙungiyar ɗalibai.

Wannan ruɗani dai ya sa rikici ya ɓarke tsakanin ɓangarorin ƙungiyar kare haƙƙin ɗaliban biyu.

Sakamakon haka, ƙungiyar ta kira hira da manema labarai na gaggawa don sanar da al’umma halin da ake ciki.

NANS wadda ita ce ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa ta Nijeriya da ke kare haƙƙin ɗalibai masu karatu a manyan jami’o’in Nijeriya da na ƙasashen waje an ba da rahoton kammala babban zaɓenta a ranar Asabar 3 ga Satumba, 2022, amma an ce mutum biyu sun fito a matsayin shugaba.

’Yan takarar biyu Kwamred Umar Farouq Lawal daga Jami’ar Bayero University BUK da ke Jihar Kano yana ikirarin cewa shi ya zama sabon shugaban ƙungiyar, yayin da ɗan jami’ar tarayya da ke Dutse, Usman Umar Barambu, shi ma ke ikirarin cewa shi ne ya lashe zaɓen.

Ɓangaren da Usman Umar Barambu ke jagoranta an ce gwamnati ce ke goyon bayanta, yayin da sauran ƙarƙashin jagorancin Umar Farouk Lawal na Jami’ar Bayero Kano, su ne suka kwashe yawancin ɗaliban.

Wani jigo a ƙungiyar da ya halarci babban taron ƙungiyar na ƙasa ya shaida wa manema labarai cewa, wasu maƙudan kuɗaɗe na gwamnati da suka kai miliyoyin Naira da ake zargin jami’an gwamnati ne suka yi amfani da su wajen sayen masu zaɓe uku daga cikin biyar sannan suka buƙaci su sauka daga muƙaminsu domin abin da suke so.

Ɗan takara, Usman Umar Barambu na Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa kuma mafi yawansu sun yi fatali da ɗan takarar da ɗalibai suka fi so, Umar Farouk Lawal na Jami’ar Bayero.

Babban jami’in na NANS ya ce, an zubar da mutuncin tsarin zaɓen har ta kai ga waɗanda ake zargin ba su cancanta ba da aka soke sun samu masaƙa.