Rubutu da hisabin marubuta

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Yau za mu yi nazari ne a harkar rubutun adabi, wacce wata daɗaɗɗiyar hanya ta faɗakarwa da nishaɗantar da jama’a. Masana da manazarta da fitattun marubuta sun daɗe suna rubuce-rubuce game da tasirin harkar rubuce-rubuce ga ci gaban zamantakewa, al’adu, ilimi da cigaban rayuwar ɗan Adam.

Tun tsawon zamani tarihin duniya ya zo da bayanai game da hikayoyi kan rayuwar mutanen baya, domin ɗaukar darasi kan yadda suka gina rayuwar su, kurakuran su da nasarorin su. Hatta tarihin Annabawa da bayin Allah nagari da muke karantawa a littattafan addini duk suna zuwa ne da manufar koyar da darasi da faɗakarwa ga ’yan baya.

Sai dai yayin da tarihi da hikayoyin mutanen baya suka kasance labaru ne na zahiri, da masana suka tabbatar da ingancin wasun su. Rubutattun labaru na adabi ana ƙirƙirarsu ne da sigar waɗancan hikayoyin domin yin nuni cikin nishaɗi, da nufin faɗakar da masu karatu da yin hannunka mai sanda game da wasu abubuwa da ke faruwa a zahirin rayuwa ta yau da gobe.

Adabi Hausa wasu tarin rubuce-rubuce ne da aka yi su cikin harshen Hausa, a yalwace ya haɗa da karin magana, almara, waƙa, kiɗa da wasan kwaikwayo da ake yin su cikin al’adun Hausawa. Sauran nau’ikan adabin Hausa sun haɗa da adabin baka wanda yawancinsu yanzu sun kasance a rubuce, sai kuma rubutaccen adabi da ake samu a littattafan labaran nishaɗi na jan hankali da aka gina wasun su daga salo irin na tatsuniyoyin adabin baka. 

Tun kafin samun ’yancin kan Nijeriya, turawan mulkin mallaka sun yi ƙoƙari wajen kafa harsashin rubutun adabi tare da wasu ‘yan bokon Arewa irin su marigayi Alhaji Abubakar Imam, marigayi Alhaji Nuhu Bamalli, Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa da sauran su, waɗanda tun a lokacin suka riqa samar da rubuce-rubuce na nishaɗantarwa da koyar da darussa na rayuwa, ta hanyar qirqirarrun labarai, ko kuma waɗanda aka fassara daga Turanci ko Larabci. 

Arewacin Nijeriya ya ƙyanƙyashe fitattun marubuta maza da mata da suka yi fice a harkar rubuce-rubuce littattafan Hausa, kama daga labaran jarumai da yaƙe-yaƙe, labaran tarihi da hikayoyin sarakuna da dauloli irin na zamanin da, labaran fatake na tafiye-tafiye da almara, zuwa labaran soyayya, da zamantakewar ma’aurata, tarbiyya da sauran rassan adabi da suka shafi wasan kwaikwayo da waƙoƙi. 

Rubutu harka ce ta ilimi da baiwa, domin ko mutum bai yi zurfin karatu ba, yana iya zama marubuci mai hikima da azancin sarrafa harshe. Don haka marubuci mutum ne mai kima da martaba musamman a idanun malamai da masu sarauta, saboda sanin da suka yi na hikima babbar kadara ce da ba kowa ke samun ta ba. Kuma ana cewa, alqalami ya fi takobi kaifi! Daga cikin marubuta ne ake samun magatakarda, sakatarori, kakaki, ko malamin makaranta. 

Dukkan waɗannan nau’ikan mutane da na ba da misalin su a sama ana samun su a cikin marubutan Hausa, har ma da waɗanda ban ambata ba na zamanin yanzu, kamar misalin masu riƙe da sarautun gargajiya, irin su Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa) shaihunan malaman jami’a irin su Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo, Farfesa Abdallah Uba Adamu, Farfesa Yusuf Adamu, da jami’an tsaro kamar tsohon jami’in ɗan sanda da ya rikiɗe zuwa ɗan jarida Bashir Yahuza Malumfashi, da masu riƙe da shaidar karramawa ta ƙasa misalin Ado Ahmad Gidan Dabino da Gwamnatin Tarayysabodaa ta ba shi shaidar OON, duk albarkacin rubutun Hausa.

Babu shakka harkar rubutun adabi ta yi albarka sosai, an samu manyan ‘yan boko, ma’aikata, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ‘yan jarida, masu harkar kasuwancin littattafai da ɗab’i da ɗalibai matasa maza da mata masu basira da kishin harshen Hausa da Arewa. Wasu ma ’ya’yan wasu marubuta ne, waɗanda iyayen su sun yi rubutun a baya, su ma kuma yanzu suna yi, irin su marubuciya Asma’u Abubakar Jasmine. 

Wani matakin nasara da yanzu marubutan Hausa suka taka shi ne na samun gidauniya ta tallafawa mabuƙata, marayu, mata da ƙananan yara, kamar irin yadda tsohuwar marubuciya Fauziyya D. Suleiman ta ke gudanarwa. Sannan kuma ga makaranta ta musamman domin koyar da sabbin marubuta dabarun inganta rubutun labari, tsara rubutun fim ko wasan kwaikwayo ta hanyar fasahar zamani, da nufin taimakawa ƙananan marubuta da ke tasowa suna buƙatar jagoranci da horo, kamar dai misalin makarantar da nima na kasance ɗalibi a cikin ta wato Kwalejin Marubutan Hausa (Hausa Writers College). 

Wannan babban abin alfahari ne da yabawa yadda marubuta suke ƙoƙarin ba da gudunmawa ga cigaban ƙasa da tallafawa rayuwar al’umma. Harkar rubutu ta tashi daga nishaɗi da ɗebe kewa kawai, ta koma jihadin samar da sauyi ga rayuwar al’ummar Arewa, duba da irin labaran da aka riƙa fitarwa daga gasar marubuta iri-iri, kan wasu matsalolin ƙasa, da kundin gajerun labarai na ɗaliban Kwalejin Marubuta Hausa, da aka yi su kan hanyoyin inganta tsaro a Nijeriya, wanda aka sanyawa suna DUKAN RUWA… 

Da ma kuma ta daɗe da zama harkar ilimantarwa ga ɗaliban makarantu, saboda littattafan da suke rubutawa don amfani da su a makarantu, tun zamanin marubuta irin su marigayi Ibrahim Yaro Yahaya na Jami’ar Bayero ta Kano, da rubuce-rubuce na koyar da sana’o’i, girke-girke, da zamantakewar aure. 

Sai dai ba za a ce haka harkar rubuce-rubucen adabi ke tafiya babu ƙalubale ba, domin kuwa tun bayan matsalar rushewar kasuwar littattafan Hausa da a baya aka yi wa laƙabi da Adabin Kasuwar Kano, saboda tasirin da ta yi wajen harkar kasuwancin littattafai, ba a samu wata matsala da ta ta ke shirin kawo zubewar mutunci da kimar harkar rubutu ba, kamar rubuce-rubucen batsa da ke neman zama barazana ga wannan daɗaɗɗiyar harka ta masu ilimi da mutunci. 

Ɓoyayyun marubuta, masu sakaya sunayensu suna rubuta labaran batsa daga maza da mata suna ɓata tarbiyyar matasa musamman ‘yan mata da yara masu tashen balaga, saboda yadda suke koya musu mu’amala tsakanin mace da namiji ta hanyar da ba ta dace ba. Ba tare da la’akari da hannun wa rubutun su zai je ba, kuma ba tare da bin tsarin doka ba. 

Sabuwar hanyar amfani da fasahar zamani ta zaurukan sada zumunta da aka fi sani da online ta bai wa marubuta da dama, zarafin cigaba da rubuce-rubuce don isar da saƙo ga masu karatun labaran da suka daɗe suna rubutawa. Ta wannan hanyar ce kuma su irin waɗannan marubuta na batsa suke fakewa su ma suna yaɗa nasu gurɓatattun labaran, ganin babu wata doka da za ta kama su, ko yadda za a gane su, ballantana wani tsari da zai tuhume su da rashin tace littattafansu. 

Kabiru Yusuf Fagge marubucin littafin ‘’ya’yanmu’ da aka fi sani da Anka, fitaccen marubuci ne daga Jihar Kano, da ya daɗe yana ba da gudunmawa ga cigaban adabi, yana ganin masu irin waɗannan rubuce-rubucen suna yin mummunan tasiri ne saboda suna fizgar mutane masu jaraba da son kawar da sha’awar zuciyarsu. Kuma hakan a cewar sa yana da illoli masu yawa, domin suna iya haifar da zina ta ruhi da ta bayyane, fitsara da gurɓata al’adun Hausawa.

Haka ita ma marubuciya Ruƙayya Ibrahim Lawal mai laƙabi da Ummu Inteesar daga Jihar Sakkwato ta bayyana takaicinta dangane da yadda irin waɗannan baragurbin marubuta ke ɓata sunan sauran marubuta masu ƙoƙarin tsaftace rubutun su. Tana mai cewa, rubutun batsa yana ragewa masu yi ƙarfin imani da tsoron Allah, kuma yana zubar da ƙimarsu a idon duniya, saboda basu san su waye za su karanta rubutun ba, ta yiwu a cikin makarantan har da ’ya’yansu, ƙanne ko makusantan da suke matuƙar so.

Akwai marubuta da dama da suka taso kuma suke ta ƙoƙarin ganin sun hana irin wannan ɗanyen aiki, don kare mutuncin su da na harkar adabi, amma abin ba ya tasiri saboda hannu ɗaya ba ya tafi, tilas sai an haɗa kai, an fuskanci matsalar da ƙarfin da ya dace cikin sautin murya ɗaya. 

Kwanan baya wata ƙungiya ta masu rubuce-rubuce a soshiyal midiya ta Arewa Media Writers reshen Jihar Filato ta gudanar da wani taro a Jos, inda aka tattauna kan hanyoyin kawo gyara a harkar rubuce-rubuce da ba su dace da tarbiyya da al’adun Hausawa ba, wasu marubuta mata Asma’u Abubakar da Rabi’atu Ahmad Mu’azu sun yi ta ƙoƙarin kare uzurin marubuta kan canja tunanin matasa masu irin wannan halayya, da kuma dakushe son karatun littattafan a wajen masu son biye musu da ba su ƙwarin gwiwa. 

Kamar yadda Malam Kabiru Yusuf Anka da Malama Sumaiyya Babayo da aka fi sani da Summie B. suka tafi kan cewa, ban da faɗakarwa da jan hankalin masu yin waɗannan rubuce-rubuce, ya kamata kuma a fahimtar da masu karatu muhimmancin ƙauracewa irin waɗannan rubuce-rubuce. Kuma hukuma ta sa doka ga duk wanda ya yi irin haka don a hukunta shi. 

A makon da ya gabata na samu halartar bikin taya murna da samun sarautar Sarkin Ɗiyan Gobir da aka naɗa wa tsohon marubuci kuma mawaƙi Aminu Alan Waƙa, ƙarƙashin ƙungiyar gamayyar marubutan Hausa, inda ɗaya daga cikin fitattun marubuta kuma na hannun daman ALA, Farfesa Yusuf Adamu marubucin littafin ‘Idan So Cuta Ne’ ya yi wata magana mai matuƙar shiga jiki da jan hankali. 

Shehun malamin adabin ya ce, Ubangiji zai yi wa kowanne marubuci hisabi kan abin da yake rubutawa, walau alheri ko sharri. Kuma al’umma ita ma tana kallonsa da gwargwadon tasirin rubutun sa ga jama’a. 

Ya kamata marubuta su gane cewa, duk abin da za su rubuta suna tunanin wata rana zai iya zama hujja a kansu, za a iya kwatancen su da abin da alƙalaminsu ya rubuta. 

A ƙarshe Ummu Inteesar ta ce, marubutan batsa su sani suna tara wa kansu zunubai ne ta hanyar wannan rubutun da suke yi. Kuma duk wanda ya karanta rubutun ya faɗa cikin wata ɓarna dalilin haka shi ma suna da kamisho. Kuma zai iya zama hujja akansu ranar gobe ƙiyama! 

Allah ya tserar da mu, kuma ya kare alƙalaminmu daga rubutun da zai jefa mu cikin fushin Ubangiji.