Rubutu hanyar zamani ce ta isar da saƙo – Oum Nass

“Ina sauya salon rubutuna kamar launin hawainiya”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Rubutu wata hanya ce ta isar da saƙo ga al’umma, ta amfani da hikima da azancin magana. Akwai marubuta da Allah ya yi wa baiwar sarrafa harshe da falsafar iya magana, kai ka ce wahayi ake yi musu. Ɗaya daga cikin su ita ce Hajara Ahmad Hussaini Maidoya, wacce aka fi sani da Oum Nass, daga ƙaramar Hukumar Haɗejia a Jihar Jigawa. Har wa yau, tana daga marubutan zube da suke cin kasuwa a harkar rubutun wasan kwaikwayo, wanda kawo yanzu wasu daga cikin rubuce rubucen da ta yi na nan ana gabatar da finafinansuu, har a shiri mai dogon zango. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana dalilin shigarta harkar rubutun adabi da nasarorin da ta samu.

MANHAJA: Ina son mu fara da sanin cikakken sunanki.

OUM NASS: Assalamu alaikum warahmatullah. Ni dai cikekken sunana Hajara Ahmad Hussain.

Gaya mana tarihin rayuwarki da gwagwarmayar karatun da ki ka yi?

An haife ni a Unguwar Kuburu a garin Haɗejia da ke Jihar jigawa. Na fara karatuna na a makarantar firamare ta Usman Bin Affan, na gama a 2004. Daga nan na wuce kwalejin ýan mata ta kwana a garin Kaugama, na kammala a shekarar 2009. An yi min aure a ranar 4 ga watan Afrilu, 2010. Yanzu Ina da yara huɗu.

A shekarar 2019 na koma karatu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Bilyaminu Usman da ke Haɗejia a Jihar Jigawa, inda na yi difiloma a ɓangaren Kididdigar Lissafi.

Menene ya ja hankalinki ki ka fara sha’awar rubutun labaran adabi?

Abin da ya ja ra’ayina na fara rubutu shine, ganin yadda mutane suka fi ɗaukar darasin rayuwa a karatun, suke kuma ganin abin da ke cikinsa kamar madubi ne da ke faruwa a rayuwar zahiri.

Kafin na fara rubutu na buɗe wani zaure na addini domin tunatar da ‘yanpuwa a tsakaninmu. Amma sai ya zamana mabiya darasin ba su da yawa, asalima sun fi mayar da hankali wajen bibiyar rubutun littattafan da suke yawo a yanar gizo.

Hakan ne ya sa na fahimci idan rawa ta sauya dole kiɗa ma ya sauya. Idan Ina son isar da saƙo sai na rikiɗe na zama ‘yar zamani. Hakan ya sa na fara da littafina na farko ‘Kowanne Tsuntsu’. Kuma Alhamdulillahi saƙon ya samu karvuwa fiye da tunanina. Zan kuma iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu, musamman da ya zama akwai wani mataccen buri na sha’awar rubutu da na ke da shi sanadin yawan karance-karancen da nake yi.

Ban da rubutun labaran hikayoyi kina kuma rubuta wasan kwaikwayo da ake shirya finafinai da su. Yaya ki ka samu kanki a wannan layin?

Yadda na samu kaina a wannan layin shi ne, zamana da marubuta na ƙungiyarmu ta Marubutan Jihar Jigawa, wato JISWA. A ciki na haɗu da Darakta Ishaq A. D. A lokacin ya turo wani fim ɗinsa mai suna ‘Ruɗani’, sai na lura akwai wasu ‘yan gyare-gyare da ya kamata a ce an yi a cikin fim ɗin, shi ne sai na ba shi shawarar yadda ya kamata inganta tsarin fim ɗin.

Hakan ne ya sa ya ji daɗin shawarwarin da na ba shi, daga bisani kuma sai ya buƙaci a kan na taya shi mu ɗora labarin, har kuma ya fara koya mini yadda ma ake yin rubutun fim. Daga nan kuma sai muka je bitar kwana ɗaya da shugaban ƙungiyar JISWA Hashim Abdallah ya haɗa mana a garin Malam Madori. Ka ji yadda na fara aikin rubuta labarin fim.

Littattafai nawa ki ka rubuta kawo yanzu?

Na rubuta littattafai za su kai 20 ban da gajerun labarai da na rubuta. Daga ciki akwai ‘Kowanne Tsuntsu’, ‘Bintu Zahra’, ‘Hanyar Bauchi’, ‘Sartse’, ‘Gudun Nasara’, ‘Haɗin Gwarmai’, ‘Yarda Da Kai’, ‘Ismaha Zainab’, ‘Inuwar Gajimare’, ‘Alhubbu Dayyi’an’, ‘Baƙar Duhuwa’, ‘Ƙawata Ce’, ‘A Barwa Rai’, ‘Ɗanyen Kasko’, ‘Jini Ya Tsaga’, sai ‘Rayuwar Nabeela’.

Kin taɓa buga wani daga cikin labarinki a matsayin littafi kuwa ko dai duk a ‘online’ suke?

A’a ban taɓa rubutawa ba, duk suna ‘online’ ne, amma akwai burin buga su ɗin a nan gaba, in sha Allah.

Kin rubuta wasan kwaikwayo guda nawa, wanne ne kuma aka fitar da shi a matsayin fim?

Guda shida na rubuta, kuma an fitar da guda uku a cikin su, su ne ‘Bikra’, ‘Ruɗani’, da ‘Farin Buri’. Ukun kuma ana kan aikin su.

Ba mu labarin fim ɗin ‘Bikra’ mai dogon zango da aka ce ke ce ki ka rubuta shi?

Fim ɗin ‘Bikra’ labari ne a kan mata masu taurin kai da ba sa jin lallashi da kuma karɓan uzuri a wurin mazajensu. Su kawai idan suna son abu to, fa a yi musu wannan abin nan take.

Wanda hakan ba ƙaramin kuskure ba ne, idan muka yi la’akari da cewar aikin gaggawa daga sheɗan ne, za a iya yin sa daga bisani a zo ana da-na-sani, kamar dai yadda ya faru ga jarumar labarin, saurinta ya zame mata nawa.
Wannan shine abin da labarin ya ƙunsa, sai dai kuma akwai wani sashi na labarin da ya faru da gaske.

Yaya ki ke kallon kanki a matsayin marubuciyar labaran hikaya ko wasan kwaikwayo?

Ina ganin kaina a matsayin wata daga cikin irin mutanen da suka yi gwagwarmaya, domin kawo sauyi a rayuwar wasu mutanen, ta hanyar isar da saƙon da zai yi tasiri a zuciyar mutane. Wanda ba ƙaramin abu ba ne mai sauƙi, dole sai ka zurfafa tunani yadda za ka yi abin da za a karɓe shi.

Ban da rubutu da tsara labarin wasan kwaikwayo, wacce baiwa kuma ki ke da ita?

Baiwar da nake jin Ina da ita, ita ce ta iya magana.

Wanne salon rubutu ki ka fi amfani da shi, rubutu ne na zamantakewa, almara, ko labarin mutanen baya?

Kamar yadda Hawainiya ba ta da launi iri ɗaya haka ni ma ba ni da tsayayyen salo. Kowanne salo Ina iya yin rubutu da shi, ba ni da salo guda ɗaya da zan ce shi nake rubutu a kansa, domin duk abin da na ga zai kawo sauyi ta wata fuskar na kan ara na yafa ta hanyar rikiɗewa na yi rubutu da shi. Ya danganta da lokacin da ya zo tunanina.

Kina shiga gasar rubutun gajerun labarai daban daban, wacce nasara ki ka samu kawo yanzu?

Alhamdulillah gaskiya na samu nasarori da yawa a gasar da nake shiga. Ta farko labarina ya yi nasarar zuwa cikin labarai goma sha biyar ɗin da aka buga a gasar Jaridar Aminiya Trust wanda suka sa a 2020 a kan jigon dambarwar siyasa. Sai kuma nasarar da labarina ya zo na ɗaya a gasar da ƙungiyarmu ta Nagarta ta sa mana iya ‘yan ƙungiyarta a shekarar 2021 kan jigon fyaɗe, inda na zo ta ɗaya.

Sai kuma gasar da ƙungiyar Arewa Media Writers reshen Jihar Filato da suka shirya gasa a kan farfaɗo da kyawawan al’adun Arewa a shekarar 2021, labarina shi ne ya yi nasarar zuwa na uku.

A yanzu kuma akwai babbar nasarar da na samu shi ne zamowa ɗaya daga cikin mutane ukun da labaransu ya yi nasara a gasar Gusau Insititute a 2022 ɗin nan.

Wanne ƙalubale marubutan adabi suke fuskanta?

Satar Fasaha. Marubuci zai sha wahala ya haɗa labarinsa daga bisani wasu su ɗauki labarin su sauya ya zamana a matsayin nasu, sai a rasa wanene ya fara rubutun tsakanin masu sata da masu shi na asali. Sai kuma masu cin kasuwar bayan fage su ɗauki labarin marubuci su ɗora a shafinsu na yanar gizo ko su karanta a YouTube ɗin su ba tare da sanin marubucin ba.

Wanne abu ne ki ka fi alfahari da shi da ya faru da ke a harkar rubutu?

Girmamawa daga mutane da dama, sai kuma zama silar haɗuwata da abokai na gari, da kuma kusanci da mutanen da a baya nake ganin sun yi mini nisa mai yawa. Amma sanadin rubutu sun zama mafi kusanci da ni.

Wasu marubutan wasan kwaikwayo na zargin masu shirya finafinai ba sa ba su ƙima da darajar da suka cancanci a ba su. Ba mu labarin yadda ki ke kallon wannan alaƙa?

Idan aka auna maganar a ma’aunin hankali zai iya yiwuwa gaskiya ne, amma kuma ta wata mahangar za a iya samun akasin hakan. Abin da na yarda da shi shi ne, mutanen da suke yi wa rubutun ne tun farko ba su gina alaƙarsu da masu ƙimar ba. Amma idan ka yi aiki da mutane na ƙwarai to, za su baka fiye da ƙimar aikinka.

Menene burinki nan gaba a rayuwarki a matsayinki ta marubuciya?

Ina son rubutuna ya zaga duniya, mutane da yawa su karɓe shi a matsayin saƙon da ke tafiya da ƙafufuwansa.

Bangon littafin ‘Ƙawata Ce’

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke ciki, kuma menene tasirin ƙungiyoyin marubuta ga cigaban su?

Ƙungiyata ita ce Nagarta Writers Association ta ‘online’. Sai kuma JISWA, wato Ƙungiyar Marubutan Jihar Jigawa.

Tasirin ƙungiya abu ne mai yawa gaskiya, za a taimaka ma wajen sanin abin da ba ka sani ba, ta ɓangaren inganta rubutunka daga kan ƙa’idojin rubutu zuwa taimaka ma da shawarwarin yadda za ka faɗaɗa wasu al’amuransa, idan hakan ya gagara a gareka, ta wata fuskar kuma sukan taimaka ma wajen yaɗa labarin naka ya isa inda ba ka je ba.

Yaya alaƙar ki ta ke da sauran marubuta, kuma su wanene ku ka fi zumunci da su?

Alaƙata da marubuta alaƙa ce mai kyau gaskiya, babu wani abu na aibu da ya tava shiga tsakanina da su. Waɗanda muka fi shiri da su, su ne waɗanda muke ƙungiya ɗaya da su, sai kuma waɗanda muka fi zama mu yi magana da su da suka zama tamkar ‘yan’uwana na jiki.

Mutane na miki kallon wacce Allah ya miki baiwar falsafa da azancin magana, a Ina ki ke samun irin waɗannan maganganu na hikima da ki ke sa wa a rubutunki?

Ita baiwa ai ba a koyonta, idan kana da ita to, kawai za ka yi aiki da ita ne. Duk lokacin da na ji Ina son yin rubutu to, kawai yana zuwa min ne nan take, ba tare da na zauna dogon tunani ba, ko na gani a wani wurin ba.

Wacce karin magana ce ta ke tasiri a rayuwarki?

Sa’a Ta Fi Manyan Kaya. Wanda ke da sa’a a rayuwa zai cimma fiye da abubuwan da tunaninsa bai kawo masa ba. Kuma duk yadda wani ya so ya dakatar da isarka zuwa ga abin to, kamar ya ƙarawa gonarka taki ne na isa ga wannan sa’arka.

Na gode.

Ni ce da godiya.