Rubutun adabin bariki ya gurɓata tarbiyyar yara da dama – Maman Amatullah

“Muna samun nasarar yaƙi da yaɗuwar rubutun batsa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A sakamakon yadda ake kokawa da cigaba da ƙaruwar marubuta labaran batsa a tsakanin marubutan adabi, waɗanda ake kira da marubuta adabin bariki, wasu marubuta sun yunƙuro domin wayar da kan marubuta da kawo sauyi a harkar rubutun adabi. Saboda haka suka kafa ƙungiyar Jarumai Writers Association, don nuna halin jarumta da jajircewa wajen nuna halayen ƙwarai da kyautata tarbiyyar matasa maza da mata ta hanyar rubuce rubucen su. Khadija Salis Ibrahim da aka fi sani da Maman Amatullah na cikin sahun gaba a wannan gangami na yaƙi da yaɗuwar littattafan batsa a ƙarƙashin wannan ƙungiya ta Jarumai. A yayin zantawarta da Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ta bayyana ƙoƙarin da suke yi, don cimma nasara a wannan gangami na wayar da kan marubuta da masu karatu. Ga kuma yadda tattaunawarsu ta kasance:

MANHAJA: Mu fara da sanin wani abu daga rayuwarki, wacce ce Maman Amatullah? 
MAMAN AMATULLAH: Assalamu alaikum wa rahamatullahi Ta’ala wa barakatuhu. 
Da farko dai cikakken sunana shi ne, Khadija Salis Ibrahim, wacce duniyar marubutan yanar gizo ta fi sani da Maman Amatullah. Ni haifaffiyar garin Kano ce, a nan na tashi, a nan na yi karatuna, sannan kuma nan na yi aure, yanzu haka ina da yarana 3.

Yaya batun karatu kuma, ko za mu iya sanin matakan da kika bi na karatu?
Eh, to. Ban yi zurfin karatu sosai ba. Alhamdulillahi, mun samu ginshiƙi mai kyau. Na fara neman ilimi tun daga gida da makarantar Islamiyya, inda na samu karatun addini, ba zan ce na gama ba, don har yanzu ana kan neman ilimi daidai gwargwado. A ɓangaren boko kuma na tsaya ne daga matakin sakandire, ko da yake akwai shirin cigaba zuwa jami’a nan ba da daɗewa ba, in sha Allahu. 

Yaya aka yi kika samu kan ki a harkar rubutun adabi?
Wannan labari ne mai tsayi sosai, amma a taƙaice dai tun tasowata na taso ne da sha’awar abin ne tun lokacin muna yara, ni da yayata. Za mu zauna tana karanta mana littattafan Hausa irin su ‘Ruwan Bagaja’, ‘Magana Jari Ce’ da sauran su. Har zuwa lokacin da nima nake karantawa da kaina a voye don a lokacin a gida ana hana mu karatun littattafan Hausa. Ba zan manta ba lokacin ina aji 6 na makarantar firamare na tava samun takarda na cewa yayata, nima ina son fara rubuta littafi. Sai ta kama yi min dariya tana cewa, an faɗa miki haka masu rubutun suke yi, babu nazari babu bincike. Na ce mata ni dai zan rubuta, kuma buga shi ma zan yi. Ta ce, Allah ya ba da sa’a. 

A lokacin na fara rubuta wani littafi da na sanya wa suna Juwairiyya. Har na yi kusan shafi goma sai na bari saboda a ɓoye na ke yi. Tun daga nan ban sake waiwayar rubutu ba har sai da na gama sakandire har ma na yi aure. Amma ko a wannan lokacin ina cigaba da bibiyar marubuta irin su Fauziyya D. Sulaiman, K/Mashi, Sa’adatu Waziri, su Hadiza Salisu Shariff har zuwa lokacin da rubutun yanar gizo ya fara yawaita.

Wata rana kwatsam a 2016 ina bibiyar wani littafi to, sai a yi ta samun jinkiri kafin marubuciyar ta yi sabon shafi, a lokacin ban san haka aikin yake da wahala ba, sai na yi ta jin haushi, ina ganin kamar tana ja mana rai ne. Sai na ke cewa wata ƙawata nima fa zan iya rubuta labarin nan. Amman kina ganin idan na yi zai karɓu kuwa? Sai ta ce mai zai hana ki gwada mana. A nan dai na samu ƙwarin gwiwar fara rubutu, don a ranar ban sauka a online ba sai da na fara rubuta wani littafi ‘Rayuwar Zainab’. Ina yin shafi ɗaya na tura mata, ta ce, kuma fa ya yi daɗi. To, haka dai na fara rubuce rubuce, ina yaɗa shi ta waya, kuma a cikin ikon Allah na fara karɓuwa.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa? 
Na rubuta lattattafai guda 10, sai kuma guda biyu da na ke kan rubuta su ba su fara fita ba. Akwai ‘Rayuwar Zainab’, ‘Haɗin Iyaye Ne’, ‘Halacci Da Mugunta’, ‘Duk Tsanani’, ‘Ɗa Na Kowa Ne’ (Rayuwar Samha), ‘A Sanadin Aiki’, ‘Hameeda’, ‘Butulci’, sai ‘Matar Mahaifina’ 1&2, da kuma ‘Na Jawa Kaina’ (Sanadin Son Jiki) 1&2.  Yanzu kuma ina kan rubuta ‘Kulu’ (Jikar Iya) da ‘Talaka’ (Bawan Allah). 

To, kina rubutun ki ne ke kaɗai ki yaɗa ko kuma kina ƙarƙashin wata ƙungiya ne? 
Eh, ina da ƙungiya. A baya na fara ne da wata ƙungiya mai suna Awesome Writers Association sai dai kuma zuwa yanzu ƙungiyar ba ta aiki. Daga baya na tsinci kaina a ƙungiyar Jarumai Writers Association ta dalilin aminiyata Basira A’D Musa (Mommy Shukura) marubuciyar littafin ‘Haɗuwar Zuciya’, wacce ita ce shugabar ƙungiyar a halin yanzu, yayin da ni kuma nake taimaka mata a matsayin Mataimakiyar Shugaba.

Menene ya bambanta ƙungiyar Jarumai da sauran ƙungiyoyin marubuta? 
Akwai ƙungiyoyin marubuta da dama, kuma kowanne suna iyaka ƙoƙarin, wajen samar da haɗin kan marubuta da samar da rubuce rubuce masu inganci, gwargwadon tsarin da kowacce ƙungiya ta ginu a kai. Sai dai mu a Jarumai, mun tsayu ne a kan yaqi da gurvacewar rubuce rubuce masu yaɗa fasadi, wato rubutun batsa da ake cewa Adabin Bariki. Saboda haɗarin da hakan ke haifarwa a tsakanin matasan mu. 

Bangon littafin ‘Matar Mahaifina’

Wanne haɗari kenan kike magana?
A gaskiya karantun irin waɗannan littattafan batsa yana haifar da illoli da dama. Rubutun adabin bariki ya canzawa yara da dama tunani, ya kuma sauke su daga kan layin da iyayensu suka ɗora su a kai na tarbiyya. Za ka ga yara masu ƙananan shekaru sun faɗa cikin mummunan yanayi ta dalilin karanta irin wannan gurɓataccen rubutu. Shi ya sa muka ga ya dace marubuta su tashi tsaye su yaƙi wannan abu da kansu, saboda sauran jama’a na yi mana kuɗin goro, suna ganin duk rubuce rubucen da muke yi, babu abin da suke koyarwa sai lalata tarbiyya. Wannan shi ne babbar matsalar da marubuta suke fuskanta a halin yanzu. 

To, ta waɗanne hanyoyi ƙungiyar Jarumai ke ƙoƙarin faɗakar da marubuta illar rubutun batsa?
Muna ƙoƙari ne ta hanyar rubuce rubucen da muke yi, da kuma ta jawo masu irin wannan rubutun na adabin bariki a jiki, muna nuna musu illar da ke cikin irin wannan rubutu da suke yi. Kuma Alhamdulillahi, ana samun nasara sosai. 

Ki na ganin akwai alamun samun nasara a wannan jan aiki da kuka sa a gaba? 
In sha Allahu, ana kan samun nasara sosai, don wasu daga cikin irin waɗannan marubutan sun fara canza akalar rubutun su, zuwa tsarin da ya dace da tarbiyya da al’adun mu na Arewa. Ka ga kuwa idan har aka rage ko aka daina rubutun batsa bakiɗaya, masu karatun ma dole su haƙura. 

Wacce shawara ce za ki bai wa matasan marubuta? 
Shawarar da nake ba su shi ne, su natsu su dinga rubutu mai ma’ana da tsari, su gujewa rubutun shirmen abin da ba zai amfanar da su ba duniyarsu da lahirarsu.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki? 
Allah wadaran naka ya lalace. Barewa ba ta gudu ɗanta ya yi rarrafe.

Mun gode.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *