Rufe kafofin yaɗa labarai: Ka hanzarta gyara kuskuren da ka aikata, kiran NUJ ga Matawalle

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), ta yi kira ga Majalisar Tsaron Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle, da ta janye matakin da ta ɗauka na rufe wasu kafofin yaɗa labarai a jihar.

Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, ƙungiyar ta ce an jiyo Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, lbrahim Dosara na cewa, kafafen da lamarin ya shafa su ne; Tashar NTA da Gamji TV da Umma TV da kuma Pride FM.

A cewarsa, an ɗauki matakin da aka ɗauka a kan kafafen ne saboda saɓa dokar aiki da suka yi, inda ya zargi tashoshin da yaɗa taron Jam’iyyar PDP a jihar.

Sanarwar ta ce a cewar Dosara, Gwamnatin Jihar ta dakatar da ayyukan siyasa a jihar saboda dalilai na tsaro, don haka wai ba a buƙatar ‘yan jarida su aiwatar da aikinsu kamar yadda dokar ƙasa ta ba su dama.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Shuaibu Usman Leman, ta nuna irin muhimmiyar rawar da ‘yan jarida ke takawa a tsakanin al’umma, musamman kuma a lokaci na dimokuraɗiyyar irin wannan.

NUJ ta tunatar da Matwalle cewa ya riƙa yin abubuwa da lura, saboda a cewarta ɗaukar irin wannan mataki ba tare da cika sharuɗɗan da suka kamata ba babu abin da zai haifar face ta’azzara matsalar tsaron da jihar ke fama da ita.

Daga nan, ƙungiyar ta ce Gwamnan ya hanzarta ɗaukar matakin gyara tare da la’akari da ‘yancin da ‘yan jarida ke da shi wajen aiwatar da harkokinsu.