Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Rufe kan iyakokin ƙasar nan ya taimaka wajen kassara harkokin kasuwancin al’ummar Arewacin ƙasar nan musamman ma jihar Kano da take cibiyar kasuwanci.
Fitaccen ɗan kasuwa ɗaya daga cikin dattawan Arewa, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ne ya bayyana hakan a Kano, inda ya ce sai da suka ja hankalin tsohon shugaban qasa Muhammad Buhari akan kar a rufe kan iyakokin nan na Arewa, suka kuma yi kira akan a buɗe bayan an rufe amma ba a ji ba sai ga shi kasuwanci ya shiga halin ha’ula’i a Kano da Arewa bakiɗaya.
Ya yi nuni da cewa hakan ta jawo su kuma hukumomin tsaro ko’ina sun shiga suna kame-kame da an ganka da kaya, inda ya ce hakan ya daɗa taimakawa kassara kasuwanci a cikin gida ma harkar na neman gagara.
Ya ce ya kamata ‘yan kasuwa na Arewacin ƙasar nan a tashi tsaye a kawo gyara akan harkokin kasuwanci da masana’antu wanda duk sun durƙushe, “wanda suke yin alawa da biskit ma sun koma sai a Kudu ake yi, masaƙu da ake yadi da atamfofi duk an rufe su.”
Gambo Ɗanpass ya ce abinda ya sa ƙasar Chana da Indiya suka bunƙasa a duniya daga masaqu ne daga nan suka bunƙasa fannoni da dama.
Ɗanpass ya ce dole ci gaban ƙasa a duniya sai an bunƙasa masana’antu da zai havaka kasuwanci.
Alhaji Gambo Muhammad ya yi kira ga ‘yan kasuwa su miƙe tsaye wajen jan hankalin shugabanni domin gina ci gaban kasuwanci domin zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.
Ya ce a baya sun zauna da shugabannin siyasa irin su Sanata Kawu Sumaila da ɗan majalisar tarayya na Rano da Kibiya da Bunkure sun gaya musu halin da Arewa ke ciki a kasuwanci don su yi abinda ya kamata.
Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ya yaba wa ‘yan majalisa akan ƙin amincewa da suka yi da buƙatar Shugaban Ƙasa na tura dakarun Nijeriya su yaƙi ƙasar Nijar, ya ce “hakan abu ne mai kyau.”