Rukuni na bakwai na maƙalallun ‘yan Nijeriya a Sudan ya isa Abuja

A halin da ake ciki, kashi na bakwai na jigilar ‘yan Nijeriyar da suka maƙale a Sudan ya isa Babban Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Manhaja ta kalato cewar, rukunin mai ɗauke da mutum 136, ya isa Abuja ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe a ranar Laraba.

Hukumar Bada Agajin Gaggawa (NEMA) ta ce wannan shi ne jirgi na 11 da aka yi jigilar maƙalallun ‘yan Nijeriya a Sudan zuwa ƙasarsu.

Ta ƙara da cewa, tun bayan ɓarkewar rikici a ƙasar Sudan, baki ɗaya an yi nasarar kwaso mutum 2,002 da ya ƙunsje maza da mata, ƙananan yara da mata masu juna-biyu, daga ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *