Rundunar JBPT ta kama haramtattun kayayyaki na N61

Daga AISHA ASAS

A ci gaba da yaƙi da harkar fasa-ƙwauri da take yi a sassan ƙasa, Rundunar Haɗin Gwiwa ta Joint Border Patrol Team (JBPT) rukuni na 3 a jihar Kwara, a cikin makonni 3 ta fatattaki ‘yan fasa-ƙwauri tare da ƙwace tarin kayayyaki wanda a ƙiyasce kuɗinsu ya kai Naira milyan N61.

Kazalika, randunar ta samu nasarar daƙile wasu baƙin haure masu shiga ƙasa ba a bisa tsarin da doka ta shimfiɗa ba.

Daga cikin tarin kayayyakin da rundunar ta kama, har da shinkafar ƙetare buhu 1,274, motoci tokumbo guda 23, ƙaramar bindiga ƙirar gida da alburusai guda 8, manyan jarkoki ɗauke da fetur guda 242, sai kuma babura guda 7 da dai sauransu.

Yayin da yake bayani ga manema labarai, Kodinetan Rundunar ta JBPT, Comptroller Oluboyega Peters, ya gargaɗi masu harkar fasa-ƙwauri da su tuba sannan su kama harkar kasuwanci mai tsafta.

Haka nan, ya ja kunnen masu taimaka wa ‘yan fasa-ƙwauri wajen shigo da kayayyakin da aka haramta cikin ƙasa da su daina.

A ƙarshe, Peters ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su zamo masu taimaka wa jami’ansu da muhimman bayanai domin cim ma nasara a harkokinsu.