Daga USMAN KAROFI
Rundunar haɗin kai ta sojojin Nijeriya da ke Arewa maso Gabas ta haramta amfani da jirage marasa maƙuka (drones) a yankin. Air Commodore U. U. Idris, kwamandan rundunar ta sama, ya bayyana hakan a wata sanarwa, yana mai cewa amfani da jiragen ba tare da izini ba na barazana ga tsaro a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.
Sanarwar ta nuna damuwa kan yadda hukumomin gwamnati da masu zaman kansu ke amfani da jirgi marar matuƙi ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba.
Kwamandan ya ce an sha samun rahotannin ganin jiragen da kuma amfani da su ba bisa ƙa’ida ’ida ba a wannan yankin. A ranar 7 ga Janairu, 2025, wani fasinja a jirgin wata kungiya mai zaman kanta daga Maiduguri zuwa Monguno an kama shi da irin wannan jirgin. An kwace jirgin din, kuma bincike yana ci gaba.
A cewar Air Commodore Idris, rundunar sama ta OPERATION HAƊIN KAI (AC OPHK) ita ce ke da alhakin sa ido da tsara ayyukan jirage a wannan yanki don tabbatar da tsaro da lafiyar duk masu amfani da sararin samaniyar jihohin Borno, Yobe, da Adamawa. Sanarwar ta jaddada cewa duk wanda ya karya wannan doka, ko da ya kasance abu mara muhimmanci, za a dauki mataki mai tsauri a kansa. Haka kuma, an yi kira ga duk masu ruwa da tsaki su kiyaye wannan doka domin tsaron kowa.