Rundunar sojan ƙasar Sin ta gamsu da sakamakon atisayen soja da ta yi a yankin teku dake gabashin zirin Taiwan

Daga CMG HAUSA

Da misalin ƙarfe 1 na yammacin yau ne, rundunar ’yantar da jama’ar ƙasar Sin dake gabashin ƙasar, ta ƙaddamar da harbe-harbe daga nesa yayin atisayen soja kan yankin teku dake gabashin zirin Taiwan.

Rahotanni na cewa, rundunar ’yantar da jama’ar ƙasar Sin, ta gudanar da muhimmin atisayen sojan ne daga ƙarfe 12 na ranar yau Alhamis zuwa ƙarfe 12 na ranar 7 ga watan Agusta.

Mai Fassarawa: Maryam Yang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *