Rundunar Sojan Nijeriya ta soma bincike kan kisan ɗan sanda a Legas

Daga BASHIR ISAH

Rundunar Sojan Nijeriya ta kafa kwamitin musamman don gudanar da bincike kan matuwar wani ɗan sanda da ake zargin soja ne ya kashe shi yayin rashin jituwar da aka samu tsakanin ‘yan sanda da sojoji a Legas.

Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a na 81 Division, Manjo Olaniyi Osoba ne ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a.

Manjo Osoba ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa ta’aziyyar Rundunar Sojan Nijeriya ga iyalan marigayin, tare da ba da tabbacin rundunar za ta yi bincike domin gano haƙiƙanin gaskiyar abin da ya faru.

Baya ga nuna takaicin rundunar dangane da kisan, Manjon ya ce rundunar ta riga ta tuntubi Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas don tattauna yadda za a shawo kan lamarin da kuma hana aukuwar makamancin haka a gaba.

Sanarwar ta ce, “An ja hankalin 81 Division zuwa ga wani labari da aka wallafa a intane game da abin takaicin da ya faru tsakanin sojoji da ‘yan sanda a yankin Ojo a Legas wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗan sanda.

“Haka nan, rundunar ta kafa Kwamitin Bincike don gudanar da bincike kan abin takaicin da ya faru.

“Duk wanda aka samu da hannu a kisan a karshen binciken, za a tabbatar da ya fuskanci ladabtarwa yadda ya kamata..,” inji Manjo Osoba.