
Daga BALA MUHAMMAD
Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa, jami’an soji sun yi nasarar kama mutum 47 da ake zargi da satar turakun hanyar jirgin ƙasa a yanki Kakau Daji, a anguwar Ayaba da ke ƙaramar hukumar Chikun na jihar Kaduna.
Mataimakin kakakin rundunar na yankin, Laftanal Musa Yahaya, ya ce jami’ansu sun kama waɗanda ake zargi ne a lokacin da su ke gudanar da wani zagaye a ranar 26 ga watan Yuni, 2024.
Ya ce, waɗanda ake zargin sun cika motoci guda biyu da kayayyakin turakun hanyar yayinda aka kama su, sannan binciken su ya ce, wani mai suna Alhaji Babawo ne ya ɗauke su aikin wanda shi ma yana shirin cika wata mota da kayan domin zuwa jibge su a wani juji da ke kusa da yankin inda jami’an suka riske su.
Har’ilayau, jami’an sun gano cewa wasu daga cikin kayayyakin da aka sace, suna jibge a wani juji, sannan suna cigaba da ƙoƙarin kamo jagoran waɗanda suka aikata ta’asan.