Rundunar sojoji sun tabbatar da mutuwar Shugaban mayaƙan ISWAP, Al-Barnawi

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Kwamandan rundunar sojojin Najeriya ya bayyana cewa, Jami’an Sojin Najeriya sun kashe Shugaban ƙungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP, wato Abu Musab Al-Barnawi.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban Jami’an tsaro, Janar Lucky Irabor. Wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ranar alhamis ɗin da ta gabata a A birnin tarayyar Abuja.

Kodayake, Janar Irabo bai bayyana ainahin cikakken bayani a kan yadda jami’an suka aike da shugaban ‘yan ta’addan barzahu ba. Amma ya ce: ” zan iya ba ku tabbacin cewa Al-barnawi dai tasa ta ƙare, kuma ya mutu shikenan.”

Shi dai Al-Barnawi, Ana kyautata zaton shi babban ɗa ne ga mutumin da ya fara ƙirƙirar aƙidar Boko Haram, wato Muhammda Yusuf. Wanda ya mutu yayin da yake tsare a hannun jami’an tsaro a shekarar 2009.

Su ma a nasu ɓangaren, mayaƙan ƙungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP, waɗanda suka yi ƙaurin suna wajen kai hare-hare i zuwa ga hukumomin tsaro, har yanzu ba su yi bayanin da yake nuna cewa Sojojin Najeriya ne ke da hannu wajen kisan Al-Barnawi ba. Har dai i zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoton ba wani bayani.

Ita dai ƙungiyar ISWAP da shi Abu Musab Al-Barnawi yake shugabanta, an samar da ita ne a shekarar 2016 bayan da aka samu saɓani da tsagin tsohon shugabanta Abubakar Shekau da kuma masu biyayya ga ƙungiyar ISIS. Inda tsagin na su Barnaiwi ɗin ya janye jiki daga Boko Haram ya samar da ISWAP.

Ita ma ƙungiyar Boko Haram ana zarginta da yin ta’adin rayukan al’umma fiye da dubu talatin a arewa maso gabacin ƙasar nan. Da kuma raba wasu fiye da miliyan biyu da gidajensu tun daga shekarar 2009 da suka fara kai hari zuwa yau.