Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban jami’an sojojin ƙasa (COAS) Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya amince da naɗe-naɗen wasu manyan jami’ai a ofisoshi daban-daban na rundunar.
Kakakin sojojin ƙasa, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce shugaban sojojin ya yi hakan ne don inganta harkokin gudanar da ayyukansu.
Ya ce an kuma sauya wa waɗansu jami’ai wuraren aiki a ƙoƙarin rundunar na daƙile matsalolin tsaro da ake fuskanta a ƙasar.
Jami’an sun haɗa da manyan jami’an hedikwatar rundunar (PSOs), Kwamandodin sansanonin horarwa, Janarorin jami’ai na GOCs, Kwamandodin Birget-Birget da suaran su.
Jaridar ‘News Point Nigeria’ ta ruwaito yadda rundunar ta yi naɗe-naɗen da sauye-sauyen. Don neman ƙarin bayani, za a iya ziyartar adireshi kamar haka: https://newspointnigeria.com/full-list-major-shakeup-in-army-as-coas-appoints-new-psos-gocs-others/