Rundunar Sojojin Nijeriy ba ta ɓangaranci ce ba – Janar Ali

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Manjo Janar Ibrahim Ali, Kwamandan Operation Safe Heaven (OPSH) mai wanzar da zaman lafiya a Filato da kewaye, ya ce, sojoji za su kasance na al’umma da kuma yin adalci ga kowa wajen tabbatar da tsaron ƙasa.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, tawagar ta OPSH tawaga ce da ke da alhakin tabbatar da tsaro da rayuka da dukiyoyi a Filato da Bauchi da kuma wasu sassan kudancin Kaduna.

An kafa ta ne a shekarar 2010 kuma ta ƙunshi Sojojin Nijeriya na Ruwa, Sama, Jami’an ’yan sanda, jami’an NSCDC da jami’an tsaro na farin kaya (DSS), ɓangaren ’yan sanda ya ƙunshi ’yan sandan tafi da gidanka da kuma ofishin bincike na musamman (Special Investigation Bureau). SIB).

Ali, wanda kuma shi ne babban kwamandan runduna ta uku na rundunar sojojin Nijeriya, Rukuba, kusa da Jos, ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi tawagar Cibiyar Tattaunawar jin ƙai ta kai masa ziyara a ranar Laraba a Jos.

Ya ƙara da cewa, OPSH ta ɗauki dabaru don kawar da ɗabi’un tashin hankali da ka iya haifar da ruɗani a cikin al’umma.

Ya ci gaba da cewa, aikin ba shi da hurumin cin zarafi da take haƙƙin ɗan Adam, ya ƙara da cewa, manufarsa ita ce samar da ingantaccen yanayi don tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

Ali, wanda ya yabawa tawagar bisa rawar da ta ke takawa wajen daƙile rikice-rikice a cikin al’umma, ya ce, taron zai ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninta da sojoji musamman a fannin musayar bayanai da kuma ɗaukar matakan gaggawa kan barazanar tsaro.

Tun da farko, shugabar tawagar, Misis Olufemi Domkap, ta yaba wa OPSH bisa yadda ta ke mayar da martani ga barazanar tsaro bisa sahihin bayanan da ta bayar.

Ta ce, tawagar ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen yin tasiri ga rayuwar masu tayar da zaune tsaye a cikin al’umma domin rungumar zaman lafiya da zumunci a tsakanin ƙabilu da addinai daban-daban.

Domkap, duk da haka, ya bayyana buƙatar ƙarfafa ƙarfin mata don haɓaka zaman lafiya a yayin warware rikici.

Ta yi kira da a horar da sarakunan gargajiya a fannin sasantawa da magance rikice-rikice, inda ta ƙara da cewa, idan al’ummomi suka rungumi hanyar sasanta rikicin cikin gida za a iya samun zaman lafiya na dindindin.