Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta haramta kowane irin nau’i na zanga-zanga a faɗin jihar.
Da yake sanar da wannan doka a jihar a ranar Litinin, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Husaini Gumel, ya ce dokar ta fara aiki nan take.
A cewar Kwamishinan, bayanan sirri sun nuna jam’iyyun NNPP da APC a jihar na shirin gudanar da zanga-zanga dangane da zaman kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar.
Idan ba a manta ba, Jam’iyyar APC a Kano ta shigar da ƙara kotu inda take ƙalubalantar bayyana NNPP da hukumar zaɓe INEC ta yi a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a a ranar 18 ga Maris da ya gabata.
Kuma waɗanda ƙarar ta shafa su ne hukumar INEC da Kabir Yusuf da kuma jam’iyyar NNPP.