Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta gayyaci zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai

Daga RABIU SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Muhammad Yakubu, ta gayyaci zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala, Hon Aliyu Sani Madakin Gini.

Wannan bayanin na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar tare kuma da raba wa manema labarai a ranar Laraba.

A cikin sanarwar kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce hukumar ta gayyaci Madakin Ginin ne bisa zargin sa da yin amfanin da bindiga yayin yaƙin neman zaɓensa da ya gudana kwanan baya.

Sanarwar ta kara da cewa, ya zuwa yanzu Madakin Gini yana sashen binciken manyan laifuffukan na rundunar a hedikwatarta da ke Bampai cikin birnin Kano inda ake zurfafa bincike.