Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta samu ƙarin kayan aiki

Daga RABIU SANUSI a Kano

Rundundar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu wasu muhimman kayan aiki da za a yi amfani da su wajen Gudanar da zaɓen gwamna a jihar.

Daga cikin kayayyakin da Rundundar ta samu sun haɗa jirgin sama mai saukar ungulu wanda zai riƙa shawagi yayin zaɓen.

Haka nan, akwai ƙarin jami’an ‘yan sanda da kuma motoci da sauransu.

Rundundar ta tabbatar wa al’ummar Jihar Kano cewa babu wani mutum da zai samu damar haddasa cikas a yayi zaɓen.

Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba, ya buƙaci rundunar ta yi aiki da kayayyakin yadda ya kamata don cimma manufar samar da su.