Rundunar ‘yan sandan Katsina ta halaka ɓarayin daji biyu da karɓe makamansu

Daga RABIU SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta yi nasarar kashe wasu ‘yan ta’addan daji guda biyu tare da samun bindiga ƙira AK-47 guda biyu haɗi da sauran wasu kaya daga maharan.

Wannan na ɗauke ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah ya fitar wa manema labarai jiya Alhamis.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana cewa, a ranar 2 ga Maris ɗin wannan shekarar jami’an su  samu bayanai cewa ‘yan ta’addan daji sun shiga ƙauyen Yasore dake ƙaramar hukumar Batsari tare da yin harbi kan mai uwa da wabi.

Cikin yardar Allah kamar yadda sanarwar ta ce, DPO mai kula da shiyyar Batsari nan da nan ya haɗa jami’an tsaro da ‘yan banga zuwa yankin da abin yake faruwa.

Sannan kuma zuwansu ke da wuya suka fara musayar wuta da ‘yan bindigar tare da samun nasarar fatattakarsu, bayan rantawa a na kare da maharan suka yi ne jami’an suka fara duba  yankin nan take suka samu gawar ‘yan ta’addan guda biyu tare da samun bindiga guda biyu tare da gidan aje harsashi guda biyar dake ɗaukar kimanin harsashi 97 da harsashin AK47 mai rai.

Sauran kayan sun haɗa da wayar hannu ƙirar Itel guda biyu, sai ɗaurin guraye, sai wata jaka da cikinta ke da Naira 2,580 tare da leta ta kunna wuta ko taba da biro da veil launin bula.

Kazalika sanarwar ta ƙara bayyana batun cewa babu shakka maharan sun ari ƙafar zomo ne da munanan raunika a jikinsu, wanda ya sa jami’an tsaro ƙara duba ko’ina a kusa don tabbatar da ko da suna nan.

Saboda haka ne ma rundunar ‘yan sandan ta roƙi mazauna yankin da su kawo sanarwar duk wanda suka gani da rauni a jikinsa madamar an tabbatar da hakan.

Daga ƙarshe kwamishinan ‘yan sandan Jihar Katsina CP Yusuf Kolo ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaron da ‘yan banga bisa ƙwazo da suka nuna yayin gaba da gaba da ‘yan tada ƙayar bayan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *